CBN zai na sayar wa 'yan canji dala akan Naira 1,590 / Hoto: Reuters

Babban Bankin Nijeriyya, CBN ya amince ya sayar da ƙudin dala ga 'yan canji don biyan buƙatun kasuwar hada-hadar kudi ta bayan fage.

CBN ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X mai ɗauke da sa hannun Dakta W.J Kanga babban Darakta a sashin Kasuwanci da hada-hadar kudade na CBN.

Sanarwar takardar mai ɗauke da kwanan watan Satumba 25 ta bayyana cewa, CBN ya amince ya sayar da dala dubu 20 ga kowane ɗan canji akan farashin Naira I,590.

“Wannan sanarwa ce ga 'yan kasuwar canji (BDCs) da kuma sauran jama'a cewa CBN zai samar da ƙarin kuɗaɗe a wannan ɓangaren na kasuwar canjin kuɗaɗen waje,'' a cewar sanarwar Babban Bankin.

''Don haka, CBN ya amince ya sayar da dala dubu 20 ga kowane ɗan kasuwar canji akan farashin Naira 1,590, don biyan buƙatun hada-hadar kasuwa,'' in ji CBN.

Yana mai ƙari da cewa, CBN ya baiwa dukkan 'yan canji na BDCs damar sayar da dala ga abokan cinikayyarsu kan farashin ribar da bai wuce kaso ɗaya cikin 100 ba bisa ga yadda CBN ya sayar musu.

''Yan canjin kasuwar da suka cika sharuɗɗan CBN, suna iya biyan Naira a cikin asusun aijiya da babban bankin ya basu.''

Kazalika, an mika shaidar saka kuɗi da kuma dukkan wasu takardu da ake buƙata don samun ƙudin CBN a sassan babban bankin a Nijeriya - (Abuja, Awka- Kano da kuma Lagos) don samun damar karbar dala dubu 20,000.

TRT Afrika