CBN zai ci gaba da ba wa gwamnatin Nijeriya kayadaɗɗen adadin kashi 5 cikin 100 na bashi a kasafin kuɗi na shekarar 2024 zuwa 2025. / Hoto: Reuters

Babban Bankin NIjeriya (CBN) ya jaddada matakin ci gaba da bai wa Gwamnatin Tarayya ƙasar kayadaɗɗen adadin kashi 5 cikin 100 na bashi a kasafin kuɗi na shekarar 2024 zuwa 2025.

Matakin dai ya yi hannun riga da gyaran ɗokar da majalisar ɗokokin ƙasar ta amince da shi a baya-bayan nan, wanda ya nemi a ƙara adadin rancen daga kashi biyar zuwa kashi 10.

Ƙudaɗe na ''Ways and Means'', lamuni ne da CBN yake bayarwa don tallafawa gwamnati domin amfani a yayin da aka samu gibi a kasafin kuɗi na wucin gadi kana suna da iyaka da matakan da doka ta shimfida.

A rahoton da aka yi masa take da 'Kudi da Bashi da Kasuwancin Waje da Ka'idodin kasafin kuɗi na shekarar 2024 zuwa 2025, wanda babban bankin ya fitar a ranarTalata', ya ce ƙa'idar ta yi daidai da na tsarin aikin Medium-Term Fiscal Framework Tool (MTFF).

A ƙarkashin shirin na MTFF, babban bankin ƙasar CBN zai sa ido kan tsare-tsare da kuɗaden da ake sa ran samu da lokuta tare da aiwatar da manufofin da suka dace tare da tallafawa shirin da zai farfado da kuma tabbatar da daidaito a attalin arzikin ƙasar.

A wani taron kwamitin majalisar dattawa a watan Fabrairun 2024, gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana cewa babban bankin ba zai sake baiwa gwamnatin tarayya lamunin ba har sai an biya bashin da aka karba a baya.

Olayemi ya bayyana cewa hakan na ɗaya dag cikin matakan da CBN ya ɗauka na dakile matsin tattalin arziki da ƙasar ta fada a ciki.

Sai dai sabbin bayanan da CBN ya fitar sun bayyana cewa, “Za a ci gaba da ba wa Gwamnatin Tarayya bashin kashi 5 cikin 100 don cike gibin ayyukan kasafin kudin da ta tara a shekarar da ta wuce.

Kana za a ba da kudin da wuri sannan a biya shi ta ko wane hali a ƙarshen shekarar da aka bayar da kuɗin."

TRT Afrika
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince