Gwamnatin ƙasar Botsawa ta ce an gano ɗaya daga cikin daimon mafi girma a ƙarkashin wurin hao ma'adinanta kuma za a baje kolinsa a ranar Alhamis.
Girman daimon ɗin ya kai karat 2,492 kuma shi ne mafi girma da aka taba gani daga kasar, sannan na biyu mafi girma da aka taba samu daga wani wurin ma'adinai a yammacin ƙasar.
Kamfanin hakar ma'adinai na Kanada Lucara Diamond Corp. ya fada a cikin wata sanarwa ranar Laraba cewa ya samo wani daimon na musamman daga ma'adinan Karowe da ke yammacin Botswana.
Lucara ya ce dutse ne mai ''inganci sosai'' kuma an same shi ba tare da wani illa ba, kana an yi amfani da fasahar X-ray wajen gano shi.
Nauyin zai iya sanya shi a matsayin dutsen daimon mafi girma da aka taba samu cikin shekaru fiye da 100 kana na biyu mafi girma da aka taɓa haƙowa daga ma'adinai bayan da aka gano nau'in dutsen na Cullinan Demon a Afirka ta Kudu a shekarar 1905.
Darajarsa ta kai dala miliyan 53
Nauyin Cullinan demon ɗin ya kai kara 3,106 kana an rarraba shi zuwa kanana duwatsu masu daraja, wasu daga cikinsu an sanya su cikin kambin sarauniyar Birtaniya.
An gano wani babban baƙin dutsen daimon ɗin a ƙasar Brazil a shekarun 1800, kana an same shi ne a saman wurin ma'adinai kuma an yi imanin cewa wani ɓangare ne na dutsen sararin samaniya.
Botswana dai, ita ce kasa ta biyu mafi girma wajen samar da duwatsu daimon kuma ita ta samar da kusan duka manyan duwatsun duniya a cikin 'yan shekarun nan.
Kafin wannan binciken dai, daimon din Sewelo, wanda aka samo a ma'adinan Karowe a shekarar 2019, an bayyana shi a matsayin na biyu mafi girma a duniya da nauyinsa ya kai karat 1,758.
Daimon ɗin Lesedi La Rona mai nauyin karat 1,111, wanda kuma aka samo daga ma'adinan Karowe na Botswana, wani sarrafa kayan ado na Birtaniya ne ya saya a kan farashin dala miliyan 53 a shekarar 2017.