Biden zai saki ganga miliyan 15 na man Amurka bayan OPEC+ sun rage kai musu mai

Shugaban Kasa Joe Biden zai sanar da zai fitar da ganga miliyan 15 ga kasuwa da ake ajje da su a ma’ajiyar man kar ta kwana ta Amurka, za a saki sosai idan har farashin makamashi ya tashi, in ji wani babban jami’in Amurka.

Jami’in ya ce sakin karin man daga ma’ajiyar man kar ta kwana ta Amurka zai zama cikamakin ganga miliyan 180 da aka saki saboda tsadar makamashi da harin da Rasha ke kaiwa Yukren ya janyo.

Umarnin da Shugaba Biden zai sanar a Laraba na nufin Shugaban zai bayyana karara gwamnatinsa ta shirya don kara sayar da albarkatun mai idan har aka ci gaba da samun tsadarsa a kasuwar duniya sakamakon hare-haren Rasha a Yukren.

Biden zai kuma bayyana cewa Amurka za ta sake sayen man don cika ma’aanarta idan farashinsa ya koma dala 62 zuwa 72 kowacce ganga, abunda masana ke cewa zai habaka samar da kaya a cikin gida ta hanyar bayar da tabbaci ko da ma farashin ya fadi.

‘Yan Democrat na samun goyon baya

Kungiyar Masu Samar da Motoci ta Amurka ta rawaito gas na zama a matsakaicin farashi na dala 3.87 kowanne galan, sama da yadda yake a ‘yan watannin da suka wuce a lokacin da saukar farashin ke bayyana shugaban da ‘yan jam’iyyarsa ta Democrata na samun karin goyon baya, bayan kuri’ar jin ra’ayin jama’a da aka gudanar.

Biden bijirewa manufofin masu samar da mai na Amurka.

Kawai sai ya zabi ya fitar da man da ake da shi a ma’jiyar man Amurka, yana kunyatar da masu sayar da shi saboda kazamar riba da suke samu, kuma ya yi kira ga samar da man da yawa daga kasashen OPEC+ da suke da bamancin ra’ayin yankunan, in ji Frank Macciarola, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasakan manufofi, tattalin arziki da gudanarwar harkoko a Cibiyar man Fetur ta Amurka.

Nan da 2050 Biden na da manufar daina amfani da man dake fitar da hayaki kwata-kwata.

Batun rage yawan man da suke fitarwa da ganga miliyan biyu a kowacce rana, ya sanya Biden zargin Saudiyya da goyon bayan Shugaban Rasha Vladiimir Putin inda ya yi alkawarin akwai sakamakon da zai biyo baya, wanda zai gurgunta farashin man a duniya.

Ganga miliyan 15 da a za a fitar ba zai biya bukatar man fetur gaba daya ta rana guda ba a Amurkıa, kamar yadda Hukumar Yada Labaran Makamashi ta sanar.

AFP