Babban Bankin Nijeriyya. /Hoto: shafin Twitter na CBN

Babban Bankin Nijeriya CBN ya fitar da sala miliyan 500 don biyan basussukan hada-hadar kudaden waje da aka tabbatar da ingancinsu a bangarori daban-daban.

Hakama Sidi-Ali, mukaddashin daraktar sadarwa ta Babban Bankin ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja a ranar Litinin.

Sidi-Ali ta ce wannan ya zo ne mako guda bayan da bankin ya biya dala biliyan biyu ga bangarorin samar da kayayyaki, sufurin jiragen sama da man fetur.

Ta ce mahukuntan babban bankin sun dukufa wajen biyan duk wasu basussukan hada-hadar kudade kasashen waje da aka yarda da ingancinsu.

Ta kara da cewa bankin CBN ya kuma fara aiwatar da dabaru da tsarin tabbatar da daidaito a kasuwannin canjin kudaden waje a gajere, matsakaici da dogon lokaci.

Ta ce "Kamar yadda gwamnan babbankin ya bayyana, CBN ya mayar da hankali ga magance muhiman batutuwa da ke kawo cikas ga ta'ammalin kudade a kasuwannin canjin kudade na Nijeriya."

Sidi-Ali ta ci gaba da cewar manufar sauye-sauye a sha'anin canjin kudaden ita ce a samar da daidaito, gaskiya da kawar da farashin kudaden kasashen waje mabambanta a kasar.

Ta bayyana tabbacin da take da shi na samar da tsayayyen farashin kudaden kasashen waje zai karfafa gwiwar masu zuba jari da jan hankalin 'yan kasuwa daga kasashen waje zuwa Nijeriya.

Ta kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da taki a kasuwar da su taka rawar da ta kamata, tare da aiki da gaskiya wanda hakan ne zai tabbatar da tsari mai inganci a kasuwar.

TRT Afrika da abokan hulda