Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya tabbatarwa da 'yan Nijeriya cewar kar su firgita inda bankin ya tabbatar da cewar dukkan kudaden da aka ajiye a bankunan kasar na nan kalau.
Sanarwar da mukaddashin daraktar ayyuka na Babban Bankin Hakama Ali ta fitar a ranar Talata ta sake tabbatarwa da jama'a kan ayyukan da suke yi na tabbatar da zaman lafiya da daidaito a bankunan Nijeriya.
Wannan cigaba na zuwa ne a yayin da jama'ar kasar a ranar Litinin suke ta raɗe-raɗi da gargadin kwastomomi su kwashe kudadensu daga wasu bankunan sakamakon ƙwace lasisinsu da babban bankin ya yi.
Sanarwar ta ce "CBN na ayyukan tabbatar da cewa bankuna sun yi aiki da ka'idojin aikin banki don tabbatar da gaskiya a tsarin ta'ammali da kudade.
"Ana yawan gudanar da bincike da gwaji don gano wane rauni da ake da shi, don taimakawa a tabbatar da ƙarfafuwar hukumomin kuɗaɗenmu."
"Dadin daɗawa, CBN din ya aiwatar da tsarin gargadi da wuri da ke riga malam masallaci wajen gani wani hatsari tare da magance shi, wanda ke ba mu damar kawar da duk wata matsala da aka gano a kan lokaci."
"Tsarin Bankin na Sanya Idanu Kan Yiwuwar Fadawa Hatsari na tabbatar da an mayar da hankali ga dokokin da aka kafa wa hukumomin kudi da za su iya kawo wani hatsari ga sha'anin kudi a kasar.
"Wannan aiki na bayar da dama wajen samar da kyakkyawan tsari tare da habaka sahihancin bankunan."
Haka zalika, CBN ya bayyana kulla yarjejeniyar fahintar juna da kasashe da dama da bankunan Nijeriya ke da rassa.
"Wannan hadin kai na inganta aiki da dokoki d atabbatar da bankunanmu sun yi aiki a karkashin dokokin aikin baki, a cikin gida da kasashen ketare"
Sanarwar ta kuma ce "CBN na mayar da hankali don samar da tsarin bankuna mai tsaro da inganci inda masu ajiya za su amince da ajje kudadensu.
"Bankin zai ci gaba da sanya idanu da tabbatar da aiki da ka'idoji don kare martabar dukkan masu ta'ammali da kudade da bayar da kariya ga tsarin bankinmu."