Babban Bankin Nijeriya ya nemi tabbatar wa masu ajiya cewa bankunan ƙasar na cikin aminci kuma kuɗaɗensu da ke ajiye a bankunan ba sa fuskantar haɗari, a daidai lokacin da ake ta ƙorafi kan matsalar rashin kudi.
Hakan ya biyo bayan rahotannin cikin gida na shawarar da mai bincike na musamman na bankin ya bai wa gwamnati na karbe wasu bankunan ƙasar, bisa zargin da ake musu cewa suna cikin hadari.
"Domin kaucewa shakku, bankunan Nijeriya suna cikin aminci," in ji Babban Bankin Nijeriya (CBN) a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X a ranar Laraba.
Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin "tsaftace" dukkan manufofin kudi a bikin rantsar da shi na watan Mayu.
A watan Yuni ne ya kori gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele tare da nada Olayemi Cardoso a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
Ba bukatar daga hankali
Babban bankin ya ce babu wani abin damuwa game da daidaiton tsarin hada-hadar kudi don haka ya bukaci abokan huldar bankuna da su ci gaba da hada-hadarsu kamar yadda suka saba.
“Muna tabbatar wa jama’a da masu ajiyar kudi game da tsaron kudadensu a cibiyoyin hada-hadar kudi na Najeriya.
Babban bankin ya ƙara da cewa, "CBN na karfafa gwiwar jama'a da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da fargabar rahotannin da ba daga CBN suka fito ba, game da yanayin amincin bankunan Nijeriya."
An samu karancin kudade a Nijeriya tun watan Fabrairu lokacin da babban bankin kasar ya gabatar da sabbin takardun kudi da aka yi wa gyaran fuska gabanin zaben kasar.
Tsofaffin takardun kuɗaɗen sun ɓace cikin sauri kuma sababbib ba su yi yawan da za su wadaci ƴan ƙasar ba.
A watan da ya gabata ne dai kotun kolin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa a rika amfani da tsofaffin takardun kudi a kasar a matsayin doka.