Babban Bankin Nijeriya ya sanar da sabbin ƙa’idojin da ya umarci bankuna a kasar su bi, a kokarin tsaftace kasuwar canjin kudin kasashen waje, wanda yake kassara darajar kudin kasar na Naira.
A wata sanarwa da CBN ya fitar ranar Laraba, dauke da sa-hannun daraktan kasuwanci da musaya, Dr Hassan Ahmed, da kuma daraktan sa-ido kan bankuna, Rita Ijeoma Sike, ya ba da umarnin fara aiki da tsarin daga daya ga watan Fabrairu.
Sabon tsarin na CBN ya daidaita yadda bankuna za su dinga bayar da rahoton mu’amalarsu da kudaden kasashen waje, inda ya fitar da sabon fam na bai-daya da kowane banki zai cika don kawo rahoto.
Babban bankin ya koka kan yadda bankunan Nijeriya suke yawaita mu’amala da kudaden kasashen waje, wanda ya yi zargin yana janyo karuwar yawan kudaden kasashen waje da bankunan suke ajiyewa a lalitarsu na tsawon lokaci.
CBN ya kayyade yawan adadin kudaden kasashen waje da kowane banki zai rike, zuwa kashi 20 cikin dari, idan an kwatanta da adadin jarin da masu hannun jari suke da shi a banki.
Yunkurin dai yana kokarin hana bankuna tafka asara sakamakon ajiye kudaden kasashen waje na tsawon lokaci, da kuma kawo sabanin lissafi wajen fayyace kudin ruwa da na biyan bashi ko takardun lamuni.
CBN ya umarci bankuna su yi amfani da nau’in kudi iri daya kan kudaden da suke bayar da bashi, da na karbar bashi, da yin jingina domin daidaito. Hakan zai sa su kaucewa matsalar bambancin farashin canjin kudi yayin da rata ta sauya.
A karshe, babban bankin na Nijeriya ya yi gargadin cewa kaucewa bin wannan umarnin zai janyo saka takunkumi kan bankin da ya saba, ko dakatar da banki daga hada-hada a kasuwar canjin kudi.