Rukunin Kamfanonin Dangote ya musanta rahoton da ke cewa zai riƙa sayar da kowace lita ɗaya a kan N600.
Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya fitar ranar Talata ta yi kira ga 'yan ƙasar su yi watsi da rahoton da ya ambato ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) tana cewa hamshaƙin attajirin zai riƙa sayar da kowace lita ɗaya ta fetur a kan N600.
"Muna so mu yi bayyana cewa ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) ba ƙawar kasuwancinmu ba ce kawo yanzu. Ba mu taɓa tattaunawa da ita ba a game da farashin man fetur, kuma ba ta da iko ko hurumin yin magana a madadinmu, mai daɗi ko mai tattare da ɓoyayyiyar manufa," in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, "muna kira ga al'umma su guji watsa jita-jita. Muna da hanyoyin isar da saƙonninmu waɗanda masu ruwa da tsaki suka sani."
Kamfanin Dangote ya fitar da sanarwar ce a daidai lokacin da ya sha alwashin soma sayar da man fetur a watan nan na Agusta, kamar yadda Anthony Chiejina ya shaida wa wata jaridar Nijeriya.
A baya, kamfanin ya sanar da cewa zai soma sayar da fetur a watan Yuli, sai dai ya jinkirta soma yin hakan saboda wasu dalilai da suka haɗa da tashin gobara a wani ɓangare na kamfanin, kamar yadda attijiri Aliko Dangote ya bayyana.