Bayanai sun nuna cewa an samu raguwar samar da ɗanyen mai a Ghana a shekarar 2023, da kashi 6.78 cikin ɗari, wanda ya haifar da raguwar kashi 9.2 cikin ɗari cikin shekaru huɗu na baya.
A shekarar 2023, Ghana ta samar da gangar mai miliyan 48 (48,247,036.61), idan an kwatanta da gangar mai miliyan 51 (51,756,481) da ƙasar ta samar a 2022.
An samu wannan bayanai ne daga Kwamitin Muradun Al'umma, a Rahoton Shekara-shekara game da Alkinta Albarkatun Man Fetur na 2023.
Rahoton ya nuna cewa tun shekarar 2019 lokacin da Ghana ta samu fitar da mafi fifikon yawan ɗanyen mai da ya kai ganga miliyan 71 (71,439,585), yawan ya sauka zuwa ganga miliyan 66 (66,926,806) a 2020, wanda ke nufin kashi 6.32 cikin ɗari.
Bayanan sun kuma nuna cewa yawan samar da ɗanyen mai ya ƙara raguwa zuwa ganga miliyan 55 (55,050,391) a 2021, sai zuwa ganga miliyan 51 (51,756,481) a 2022, sannan zuwa ganga miliyan 48 (48,247,036.61) a 2023.
Hakan na nufin raguwar kashi 17.75, da kashi 5.98, da kuma kashi 6.78 cikin ɗari, a shekarun na 2021, da 2022, da 2023 bi-da-bi.
Rahoton na 2023 ya tabbatar da raguwar yawan ɗanyen man da Ghana ke samarwa duk shekara a karo na huɗu a jere, tun shekarar 2010.
A Disamban 2010 ne Ghana ta fara samar da mai daga rijiyar Jubilee Field. Sauran rijiyoyi biyu da ƙasar ke samar da ɗanyen mai su ne rijiyar TEN, da rijiyar Sankofa Gye-Nyame (SGN).