Hukumomi sun ce sun rufe kamfanin Sol Cement ne  sun dauki bayan dukkan yunkurin da suka yi na karbar harajin ya ci tura./Hoto: Ghana News Agency

Hukumar Karbar Haraji ta Ghana ta rufe kamfanin siminti na kasar China, Sol Cement, saboda kin biyan haraji.

Hukumar tana bin kamfanin, wanda ke rukunin masana'antu na Tema, fiye da cedi miliyan 700.

Kamfanin dillancin labarai na Ghana News Agency ya ambato jami'in hukumar reshen Greater Accra, Mr Joseph Annan, yana cewa sun dauki matakin ne bayan dukkan yunkurin da suka yi na karbar harajin ya ci tura.

Ya kara da cewa kudaden da ake bin kamfanin sun hada da haraji da tarar da aka ci shi saboda kin biyan haraji da kudin-ruwa da kuma tarar da aka ci shi saboda bayar da takardun jabu.

Shugabannin kamfanin ba su ce uffan ba kan kulle kamfanin.

TRT Afrika