Ministan kasuwanci na Ghana Mista Kobina Tahir Hammond ne ya kaddamar da  ɓude taron baje kolin kayayyakin da ayyuka ''Bazaar" na  asalin ƙasar a birnin Accra/ Hoto: GNA

An buɗe babban taron baje-kolin kayayyaki da ayyuka na 'Made-in-Ghana Bazaar' karo na uku a Accra babban birnin ƙasar ta Ghana.

Ministan masana'antu da kasuwanci na ƙasar Mista Kobina Tahir Hammond ne ya ƙaddamar da taron a ranar Alhamis, inda ya buƙaci al'umma su tallata kayayyaki da ayyuka na cikin gida a Ghana.

An yi wa taron na kwanaki uku wanda ma'aikatar harkokin waje tare da haɗin gwiwar ma'aikatar kasuwanci da masana'antu na ƙasar suka shirya take da "Tallata Kayayyaki da ayyukan cikin gida na Ghana don Samar da Ci gaban Tattalin Arziki."

"Ina ƙarfafa kowannenku gwiwa kan ku Tallata tare da sayar da waɗannan kayayyaki da ayyuka na cikin gida Ghana, ba kawai don amfaninsu da farashinsu ba, amma don girmamawa tare nuna kishin ƙasarmu Ghana," kamar yadda kamfanin yaɗa labarai na Ghana GNA ya rawaito Mista Hammond yana cewa.

Ministan ya ƙara da cewa "Ta hanyar tallafa wa kasuwancinku na cikin gida da masu sana'a, ba kawai kuna biyan buƙatunku ba ne, kuna zuba jari a tattalin arzikinmu ne da kuma alkinta sassanmu masu amfani ga al'ummomi masu zuwa,''

Hajar ta Ghana wato "Made-In-Ghana Bazaar" zai mayar da hankali ne kan ɗaura kayayyakin Ghana a kan sikelin duniya ta hanyar dangantakar diflomasiyyar ƙasar da kasashen duniya. / Hoto: GNA

Taron baje kolin kayayyakin 'Made-in- Ghana Bazaar' ya ƙunshi abubuwa daban-daban fiye da 150 waɗanda suka haɗa da ƙirƙire-ƙirƙiren fasahohi da sana'o'in gargajiya da kuma ayyukan masana'antu da suka haɗa da fasaha ta zamani da dai sauransu.

''Duk wata sayayya da aka yi a nan za ta taimaka wajen samar da ci gaba ga rayuwa da kuma inganta yawan aiki da ɗorewa a cikin al'ummominmu," in ji Ministan.

Hajar ta Ghana wato "Made-In-Ghana Bazaar" zai mayar da hankali ne kan ɗaura kayayyakin Ghana a kan sikelin duniya ta hanyar dangantakar diflomasiyyar ƙasar da ƙasashen duniya.

A shekarar 2018 ne aka ƙaddamar da wannan gagarumin shiri ƙarƙashin ma'aikatar harkokin wajen kasar da haɗin gwiwar yankuna, biyo bayan matakin da gwamnati ta ɗauka na sake kafa ofishin kula da tattalin arziki, cinikayya da kuma zuba-jari na ma'aikatar a shekarar 2017 ƙarkashin shirinta na kawo sauyi a fannin tattalin arziki da masana'antu.

Tun daga shekarar 2017, gwamnatin Ghana ƙarƙashin jagorancin shugaba Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ta haɗa kai da kamfanoni masu zaman kansu, wajen haɓaka ayyukan masana'antu tare da faɗaɗa hanyoyin kasuwanci, musamman a sassan da ke da alaƙa da sarrafa albarkatun ƙasa.

''Wannan yunƙuri wani ɓangare ne da ke cikin manufofin sauyi na Masana'antu wanda ya ba da fifiko ga ƙara samar da hanyoyin shigowa da kuma fitar da kayayyaki, wanda sakamakon hakan ya ke ƙara darajar mu," in ji Mr Hammond.

TRT Afrika da abokan hulda