Hukumar da ke yi wa Kamfanoni Rajista a Nijeriya (CAC) ta bai wa kamfanonin da ke kasar wa'adin yi rajista kamar yadda doka ta tanada idan ba haka ba ta soke lasisinsu.
Shugaban Hukumar Hussaini Ishaq Magaji ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Juma'a a Abuja, babban birnin kasar.
Ya ce dokokin kasar sun bukaci duka kamfanonin da ke kasar su rika samar da bayanai abubuwan da suka shafe su “ko sauyin adireshi ko sauyin kasuwanci da sauransu, sannan kamfanin ya biya wasu kudi da ba su taka kara sun karya ba.”
“Doka ta bukaci duk shekara kowane kamfani ya cika ka’idoji. Duk wanda bai cika ba, to doka ta ba hukumar CAC damar cire sunan wannan kamfanin daga tsarinta,” in ji shugaban CAC.
Hussaini Ishaq Magaji ya ce sun bai wa kamfanoni zuwa ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa don su tabbatar sun cika ka’idodin da doka ta tana kan kamfanoninsu.
A karshe shugaban ya yi gargadi ga “kamfanonin tafiye-tafiye musamman masu yin aikin Umrah da Hajji da kamfanonin hakar ma’adinai da kamfanonin canjin kudin ketare da aka yi wa rajista wadanda ba su gyara takardunsu ba da su yi hakan.”