Yawan kasuwanci tsakanin Turkiyya da Afirka ya karu zuwa dala biliyan $40.7 a 2022, daga dala biliyan $5.4 a 2005. / Hoto: DEIK

Daga Hamza Kyeyune

Hadin kai tsakanin Turkiyya da Afirka ya samu habaka sosai tun bayan da gwamnatin kasar ta samu damar zama mamba 'yar kallo a Tarayyar Afirka, a 2005.

Wannan hadin-kai na cude-ni-in-cude-ka da ya zama jigon manufofin Turkiyya a kasashen waje, ya kawo nasarar da ta kai ga sama da kasashen Afirka 40 suka kafa ofisoshin jakadanci a Ankara.

Wannan nasara ta diplomasiyya ta kuma bayar da damar karuwar yawan jarin kasuwanci tsakanin Turkiyya da Afirka, wanda ya haura na tsakanin nahiyar da Amurka a 2022, inda ya kai dala biliyan $40.7 daga dala biliyan $5.4 a 2005.

An yi hasashen wannan adadi zai kai dala biliyan $50 bayan an tattara bayanan shekarar da ta gabata, kamar yadda Hukumar Huldar Kasuwanci da kasashen waje ta Turkiyya (DEIK) ta bayyana.

A wajen taron Kasuwanci na Turkiyya-da-Airka da aka gabatar a watannin baya a Istanbul, shugaban Hukumar DEIK Nail Olpak ya ce manufarsu ta farko ita ce habaka jarin kasuwancin dala biliyan $50 kowace shekara, sannan ya kai zuwa biliyan 475.

Duba da maudu'in taron na - "Magance kalubale, da fito da damarmaki: Gina Kakkarfar Alakar Cigaban Tattalin Arzikin Turkiyya-da-Afirka" - Olpak ya bayyana cewa hanyar samun mafita ita ce a gina karin sabbin gadoji na hadin-kai tare da kawar da shingayen da ke hana cimma manufa iri guda.

Ministan Kasuwanci na Turkiyya Omer Polat kuma ya bayyana cewa dagewar da aka yi wajen tabbatar da cigaban alakar na bayyane karara, a yawan adadin jarin da ke tsakanin Turkiyya da Afirka, wanda ya ninka sau 7.5 tun bayan da aka ayyana niyyar habaka alakar kasuwanci da nahiyar a 2003.

Ya kara da cewa Zuba jarin Turkiyya a Afirka ya kai dala biliyan $10, kuma masu zuba jari na Turkiyya na samar da ayyukan yi ga dubunnan daruruwan 'yan Afirka.

Samar da kayayyakin more rayuwa

Kamfanonin Turkiyya na fadada ayyukansu wajen yin gine-gine a Afirka, inda ake ganin 'yan kwangilar kasar da suke zama manyan abokan gogayyar kamfanonin kasashen waje da ke nahiyar.

Manyan kamfanonin gine-gine na Turkiyya irin su Yapi Merkezi da ke Istanbul, sun gudanar da ayyuka da dama a Afirka, kuma suna gina gidaje, da filayen wasanni, da manyan dakunan taro, da asibitoci, da manyan kantinan saye da sayarwa.

A farkon 2023, gwamnatin Uganda ta kulla yarjejeniya da Yapi Merkezi don gina layin dogo na Uganda mai tsayin kilomita 273, wanda ya tashi daga iyakar Malaba zuwa babban birnin Kampala, kan kudi dala biliyan $2.2.

Da fari an shirya kamfanin Harbour Engineering na China ne zai gina layin dogon. Bayan shekaru takwas ba a fara ba, sai Uganda ta zabi Yapi Merkezi na Turkiyya don gudanar da aikin.

Wannan kamfani na Turkiyya ya kuma samu aikin kwangila a Habasha, wadda ya daga kasashen Afirka da ke habaka cikin gaggawa, don gina layin dogo mai nisan kilomita 3,910, da gadoji 51 da hanyar karkashin kasa 12, da gadojin sama na jirgi 14, da titin karkashin kasa guda daya.

Wannan hanya na da muhimmanci ga Habasha wadda ba ta da gabar teku, inda hakan zai ba ta damar saduwa da hanyoyin kasuwanci ta Mashigar Bab al Mandab.

Yapi Merkezi ya kuma samu aiki a Tanzania don gina layin dogon da zai hade Darussalam da Morogoro, wanda zai bai wa jirgin kasa damar gudun kilomita 160 a awa daya, da kuma wani layin dogon da zai hade Jumhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Uganda zuwa Tekun Indiya.

Wadannan ayyuka, idan aka hade su sun kai na dala biliyan $3, kuma hakan na nufin kamfanonin Turkiyya na kalubalantar kamfanonin Yammacin duniya da suka mamaye Afirka.

Kamfanonin Turkiyya sun kuma gina Babban Wajen Taro na Tarabulus a Libiya, da Babban Wajen Taro na Kigali, a Rwanda, da ginin Majalisar Dokokin Kamaru, da kuma Dakar Arena da ke Senegal, da ke da wajen zaman mutane dubu 15,000.

Akwai kuma manyan ayyuka kamar babban Dakin Taro na Kasa da Kasa na Dakar, da Filin Tashi da Saukar Jiragen Sama na Blaise Diagne da ke Sanagal, da Filin Tashi da Saukar Jiragen Sama na Niamey, a Nijar.

Polat Yol Yapi, wani kamfanin gine-gine na Turkiyya da ya yi suna a duniya, a yanzu haka yana gina hanyar Muyembe-Nakapiripirit mai nisan kilomita 90 da ta hada Uganda zuwa Kenya da Sudan ta Kudu da Habasha.

Kamfanonin Potenza Lubricants da Acibadem Health Care Group na daga sauran kamfanonin Turkiyya da suke bayar da gudunmawa wajen inganta harkokin sufuri a Uganda, da kula da lafiya, kuma suna samar da ayyukan yi da ke bukatar kwarewa, sannan suna bunkasa kasuwancin kasar, tare da assasa tushen habakar tattalin arziki a dogon zango.

Manyan alkaluma

Kungiyar 'Yan kwangila ta Turkiyya ta bayyana cewa kamfanonin gine-gine daga Turkiyya na gudanar da kaso 17.8 na ayyukan da kamfanonin kasa-da-kasa ke yi a Afirka.

Wannan ya kawo babban sauyi, duba da cewa manyan kwangilolin da ake bai wa kamfanonin Yammacin duniya a yanzu ana bai wa kamfanonin Turkiyya.

Alkaluman da DEIK suka fitar sun yi nuni da cewa 'yan kwangilar Turkiyya sun kammala ayyuka 1,864 a bangarori daban-daban na nahiyar Afirka, da jimillar dala biliyan $85.4.

Misali zuba jarin da kamfanonin Turkiyya suka yi a Uganda, za a iya yin sa a sauran kasashen Afirka don magance gibin kayan more rayuwa da ake da su, tare da samun cibiyoyin kasuwancin kasa da kasa da dama.

Khalid Abdallah, injiniyan gine-gine yana da ra'ayin cewa Turkiyya na da babbar dama a Afirka, saboda kusancinta da nahiyar da kuma tsarin kasuwancinta na kawo cigaba a Afirka.

Ya fada wa TRT Afirka cewa "Idan Afirka za ta yi amfani da damar hadin-kanta da Turkiyya, to za ta samu cigaban kayan more rayuwa cikin sauri, da habakar tattalin arzikinta, da makomar 'yan kasa mai kyau."

Kasuwanci da hadin-kai tsakanin Turkiyya da Afirka zai bunkasa sosai a yayin da karin kasashen Afirka, da suka hada da Masar da Habasha suka shiga kawancen BRICS a watan Janairun 2024. Ana sa ran Turkiyya za ta shiga kawancen a 2025, wanda masu nazari ke cewa hakan zai kara karfafa alakar kasuwanci a tsakanin kasashen.

TRT Afrika