Wasu hotuna da kafar yada labaran gwamnati ta wallafa a Facebook suna nuna mutune sun nuna mutane suna amfani da hannayensu wajen tono wadanda suka rayu a cikin kasa. / Hoto:Reuters

Aƙalla mutum 157 ne suka mutu sakamakon zaftarewar ƙasa a wani yanki mai nisa a kudancin Habasha a ranar Litinin, kamar yadda hukumomi suka tabbatar a ranar Talata, suna masu gargaɗin cewa adadin waɗanda suka mutu zai iya haura haka.

"Ana ci gaba da neman gawawwakin kuma ba a gano da dama daga cikinsu ba. Yankin da lamarin ya faru yana da wahalar zuwa," in ji Markos Melese, shugaban Hukumar Bayar da Aajin Gaggaa ta yankin Gof, a tattunawarsa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ya ƙara da cewa, "Kawo yanzu mun gano gawawwakin mutum 157 daga ƙauyuka biyu... Mun yi amannar cewa adadin zai ƙaru."

Tun da farko, Sashen Watsa Labarai na yankin Gofa ya ce “An gano gawawwaki fiye da 55 a zaftarewar ƙasar,” yana mai ambato jagoran yankin Dagmawi Zerihun.

Zaftarewar ƙasar ta faru ne da misalin karfe 10 na safe, bayan mamakon ruwan sama a yankin mai tsaunuka a yankin da ke Kudancin Ethiopia, a cewar Dagamawa.

Ya ce mata da yara na daga waɗanda suka mutu, yana mai ƙarawa da cewa ana ci gaba da neman waɗanda suka tsira.

Mummunan yanayi

Wasu hotuna da kafa yaɗa labaran gwamnati Fana Broadcasting Corporate ta yaɗa a Facebook sun nuna daruruwan mutane kusa da inda lamarin ya faru, sun yi buɗu-buɗu da jar ƙasa.

Hotunan sun nuna mutane suna amfani da hannayensu wajen tono waɗanda suka rayu a cikin ƙasa.

Yankin Gofa yana da kimanin nisan kilomita 450 daa babban birnin ƙasar Addis Ababa, kuma sai an yi tafiya awa 10 kafin a kai yankin daga babban birnin.

TRT Afrika