Al-Burhan da Dagalo sun fara rikici a kan karfin iko a yayin da kasar ke shirin komawa kan turbar dimokuradiyya. / Photo: Reuters

Gwamnatin Sudan ta yi maraba da matakan da kasashe makwabtanta suka dauka na kokarin kawo karshen yakin da ake yi a kasar.

A yayin wani taro a Alkahira, babban birnin Masar a ranar Alhamis, kasashe makwabtan na Sudan sun samar da wata mafita ta dakatar da yakin na Sudan.

"An amince a samar da wata tawaga ta ministoci da za ta yi zamanta na farko a Chadi don gabatar da wani tsari na dakatar da yakin tare da cimma wata sahihiyar matsaya kan rikicin na Sudan," a cewar Shugaban Kasar Masar Abdel Fattah El-Sisi a wata sanarwa.

Da yake mayar da martani a kan lamarin, kwamitin gwamnatin rikon kwarya na Sudan, karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan, ya ce: “Gwamnatin Sudan ta yi maraba da taron na makwabtan Sudan... Muna kuma mika godiyarmu ga kasashe makwabta da suka bayyana matsayarsu kan tsaro da zaman lafiyar Sudan."

Kwamitin rikon kwaryar ya ci gaba da cewa "yana jaddada kaguwarsa ta yin aiki da duka bangarori don neman dakatar da yakin tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin kasarmu baki daya."

An shirya kawo karshen yakin

Kwamitin, wanda yake da alaka da rundunar sojin Sudan, ya ce a shirye yake ya dakatar da yakin ba tare da bata lokaci ba "idan har mayakan sa kan suka dakatar da kai hare-hare gidajen mutane da unguwanni da kan dukiyoyin fararen huka da na gwamnati da tare hanyoyi da kuma sace-sace."

A yayin taron da aka yi a Alkada sauran kasashe da su "girmama 'yancin Sudan da mutunta iahira din, mahalarta sun nemi bangarorin da ke fada da juna iyakokinta."

Taron ya samu halartar El-Sisi da Firaministan Habasha Abiy Ahmed da kuma Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir.

Sauran mahalartan sun hada da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki da na gwamnatin rikon kwarya ta Chadi Mahamat Idriss Deby da na Libya Mohamed al-Menfi da shugaban kasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka Faustin-Archange Touadera.

SAF da RSF

Ana fafata yakin na Sudan, wanda aka fara shi ranar 15 ga Afrilu ne tsakanin rundunar sojin kasar ta RSF da kuma rundunar mayakan sa kai ta RSF da Mohamed Hamdan Dagalo ke jagoranta.

Al-Burhan da Dagalo sun fara rikici a kan karfin iko a yayin da kasar ke shirin komawa kan turbar dimokuradiyya.

A kalla mutum 3,000 aka kashe sannan aka raba kusan mutum miliyan uku da muhallansu tun bayan fara yakin, a cewar hukumomin gwamnatin Sudan.

TRT Afrika