Daya daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasar Ghana da za su fafata a zaɓen 7 ga watan Disamba ta mutu.
Akua Donkor, wadda ta kafa jam’iyyar Ghana Freedom Party (GFP), ta rasu ne a wani asibiti a Accra, babban birnin Ghana , ranar 28 ga watan Oktoba.
Donkor ɗaya ce daga cikin ‘yan takarar shugaban ƙasa mata biyu a zaɓe mai zuwa. Ɗayar ita ce Nana Frimpomaa ta jam’iyyar Convention People's Party (CPP).
Kamfanin watsa labaran ƙasar Ghana Broadcasting Corporation ya ce Donkor ta rasu ne tana da shekaru 72.
Matsalolin ciki
Kafafen watsa labarai a Ghana sun ba da rahoton cewa ma’aikatan jinya a wani asibitin da ke gabashin ƙasar sun gano cewa ‘yar takarar tana da matsaloli da suka shafi ciki ranar Asabar 26 ga watan Oktoba.
Bayan ta ga likita, an ba ta damar komawa gida a wancan lokacin.
Ranar Litinin Donkor ta sake kwaciya rashin lafiya da ke buƙatar taimakon gaggawa, kuma an garzaya da ita wani babban asibiti a birnin Accra domin samun kulawa ta musamman.
Mutumin da ke yin takarar mataimakinta, Kwabena Agyeman Appiah Kubi, ya ce ya ziyarci ‘yar takarar a asibiti da misalin ƙarfe ɗaya ranar Litinin kuma ya bar ta da misalin ƙarfe 3:30.
Me zai faru idan ‘yar takarar shugaban ƙasa ta rasu kafin zaɓe?
Daga baya aka kira shi ta wayar salula da misalin ƙarfe goma na dare cewa Donkor ta rasu.
Kubi, mai shekara sama da 40, mai gatabar da shirin rediyo ne a Ghana, kuma an fi saninsa da suna Roman Fada.
Dokar Ghana ta ce idan ‘yar takarar shugaban ƙasa ta mutu bayan jam’iyyarta ta tsayar da ita, hukumar zaɓe za ta bai wa jam’iyyar kwana 10 domin tsayar da sabuwar ‘yar takara.
Da zarar an tsayar da sabuwar ‘yar takarar kuma aka tantance ta, za a iya ɗaga zaɓen da kwana 21. Idan ‘yar takarar indifenda ce, ba za a sauya jadawalin zaɓen ba.
Kwanaki 37 zuwa zabe
A yau, ‘yan ƙasar Ghana suna da kimanin kwanaki 37 kafin zaɓukan 7 ga watan Disamba. Rahotanni sun ce hukumar zaɓe za ta sake buga ƙuri'u domin maye gurbinta.
A halin yanzu dai hukumar zaben tana da lokacin da za ta iya gudanar da zaɓen a daidai lokacin da aka shirya gudanar shi.
Kubi ya bayyana aniyarsa ta kasancewa ɗan takarar shugaban ƙasar Ghana a ƙarƙashin Ghana Freedom Party.
An haifi marigayiya Donkor ne a yankin Ashanti na kudancin ƙasar a watan Fabrairun 1956.
Hamshakiyar mai noman koko
Babu cikakkun bayanai game da yadda ta fara karatunta.
Daga baya dai ta zama hamshaƙiyar manomayar koko wadda ta yi sha’awar shiga siyasa.
A shekarar 2012, ta nemi ta yi takarar shugaban ƙasar Ghana a matsayin indifenda, amma hukumar zaɓe ba ta amince da buƙatarta ba domin ba ta cika sharuɗɗan takarar ba.
Bayan haka ne ta kafa jam’iyyar Ghana Freedom Party da zummar ƙwato wa marasa galihu ‘yanci.
Ta zo ta 11 a zaɓukan 2020
A shekarar 2016, an sake hana ta takarar shugaban ƙasa domin ta gaza cika sharuɗɗan takarar.
A shekarar 2020, Donkor ta cika sharuɗɗan, kuma ta kasance ɗaya daga cikin ‘yan takara 12 da suka fafata a zaɓen.
Ta zo ta 11, inda ta samu ƙuri’u sama da 5,300 a zaɓen da shugaba Nana Akufo-Addo ya yi nasara da ƙuri’u miliyan 6.7.
Tsohon shugaban ƙasa John Mahama na jam’iyyar adawa ya kasance na biyu bayan ya samu ƙuri’u miliyan 6.2.
Kare hakkin mata
A zaɓen wannan shekarar, an tantance Donkor tare da Mataimakin Shugaban ƙasa Mahamudu Bawumia, wanda ya kasance ɗan takaran jam’iyya mai mulki da tsohon shugaban ƙasa Mahama da kuma wasu 'yan takara goma.
Donkor ta kasance mai kishin noma tare da fafatuka wajen kare hakkin mata.
Abin da aka fi sani a yaƙin neman zaɓenta shi ne alƙawarin da ta ɗauka na ƙara adadin hutun haihuwa daga wata uku zuwa shekara ɗaya.
Donkor ta rasu ta bar ‘ya’ya da dama.