Rikice-rikicen da ke faruwa a Gaza da Ukraine sun yi matukar shafar tallafin kudade da ake samar wa harkokin kiwon lafiyar al'umma da kuma kananan yara a Yammaci da Tsakiyar Afirka, a cewar wani jam'in Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF.
Shugaban sashen kula da mata masu juna-biyu da jarirai da kuma lafiyar matasa na UNICEF a Yammaci da Tsakiyar Afirka Dr. Boon Alexandre ya ce kudaden da ake kashewa a fannin kiwon lafiya a yankunan sun ragu zuwa kusan kashi 50 cikin 100 sakamakon yake-yaken da ake yi.
"A duk lokacin da aka samu wani al'amari babba kamar rikicin Isra'ila da Falasdinu da kuma yakin Rasha da Ukraine, hankulan manyan kasashen duniya kamar Amurka da Birtaniya da kuma China kan karkata zuwa ga wannan batun, "kamar yadda shugaban ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu a Lome, babban birnin Togo a ranar Alhamis.
Ya yi wannan jawabi ne a yayin wani taron manema labarai da aka gudanar kan matsalolin kiwon lafiyar jama’a da abinci mai gina jiki da kuma lafiyar yara a Yammaci da Tsakiyar Afirka.
Cike Gibi
Dr. Alexander ya bayyana cewa a yanzu haka kasashen da ke bayar da agaji sun fi mayar da hankalinsu ne wajen tallafawa ayyukan jinkai a yankunan da ke fama da rikice-rikice da yake-yake.
Jami'in na UNICEF ya ce halin da ake ciki a yanzu na iya kawo tsaiko a tallafin da kasashen Afirka suke samu wajen magance matsalar rashin abinci mai gina jiki da mutuwar jarirai da sauran matsalolin kiwon lafiyar jama'a.
Ya bukaci gwamnatocin kasashen Yammaci da Tsakiyar Afrika kan su kara kasafin kudaden kiwon lafiyarsu domin cike gibin da ake samu a kudaden da kasashe masu ba da taimako suka haifar.
Taron kafafen yada labarai da aka gudanar na kwanaki uku ya samun halartar 'yan jaridu a bangaren kiwon lafiya kusan 60 daga kasashe 23 na yammacin Afirka da tsakiyar Afirka.