Rasha ta tabbatar da ziyarar da shugabannin Afirka za su kai don shiga tsakani a yakinta da  Ukraine

Rasha ta tabbatar da ziyarar da shugabannin Afirka za su kai don shiga tsakani a yakinta da  Ukraine

Kasashen Zambiya da Senegal da Jamhuriyar Congo da Uganda da Masar da kuma Afirka ta Kudu ne suka kawo shawarar hakan.
Afirka ta Kudu na daga cikin kasashen Afirka da dama da suka ki nuna bangaren da suke goya wa baya tsakanin Rasha da Ukraine a yakin da ake yi /Hoto: Reuters

Fadar Kremlin ta Gwamnatin Rasha ta ce wata tawaga daga kasashen Afirka da ke fatan gabatar da kiranta don kawo karshen yakin da ake yi tsakanin kasar da Ukraine za ta kai ziyara Moscow.

Mai magana da yawun Fadar Kremlin Dmitry Peskov ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis cewa a shirye Rasha take ta saurari "duk wata bukata" da za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Shugaban Kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da cewa wata watagar shugabannin Afirka mai mutum shida, na shirin zuwa Ukraine da Rasha "ba tare da wani jinkiri ba" don taimaka wa wajen samo mafita ga yakin.

Kasashen Zambiya da Senegal da Jamhuriyar Congo da Uganda da Masar da kuma Afirka ta Kudu ne suka kawo shawarar hakan.

Shugaban Rasha Vladimir Putin da na Ukraine Volodymyr Zelensky sun yi maraba da tsarin kuma "sun amince su karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka" a biranen Moscow da Kyiv.

Afirka ta Kudu na daga cikin kasashen Afirka da dama da suka ki nuna bangaren da suke goya wa baya tsakanin Rasha da Ukraine a yakin da ake yi.

TRT Afrika da abokan hulda