An dage zaman shari'ar shugaban 'yan adawar Senegal / Hoto: AP

An dage zaman shari'ar fyade da ake yi wa madugun 'yan adawar Senegal Ousmane Sonko da ya kamata a fara a babban birnin kasar, har zuwa ranar 23 ga watan Mayu.

Jinkirin ya biyo bayan hatsaniyar da ta barke ta tsawon sa'a 24 a ranar Talata, da ke da alaka da shari'ar da ake yi wa fitaccen dan siyasar a yammacin Afirka.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta ce mutum uku ne suka mutu, ciki har da wani dan sanda da ya mutu sakamakon buge shi da wata mota mai sulke da ke kokarin komawa ta baya.

‘Yan sanda da magoya bayan Sonko sun yi arangama a ranar Litinin a birnin Ziguinchor da ke kudancin Senegal, inda matasa suka yi ta jifa da duwatsu tare da amfani da itatuwan bishiya wajen kafa shinge a kan hanyar da ke zuwa gidan Sonko.

A rikicin, an kona motocin bas-bas a Dakar babban birnin kasar da dama, masu zanga-zangar sun yi ta jifan 'yan sanda da duwatsu, inda su kuma jami'an tsaro suka mayar da martani ta hanyar harba hayaki mai sa hawaye.

Mai shari’a kan manyan laifuka na babbar kotu da ke Dakar ya dage shari’ar Sonko don bai wa lauyoyi damar gabatar da manyan shaidu a yayin tantance bayanan kotun.

Zaman gidan yari har tsawon shekara 10

Ana zargin Sonko da yin lalata da kuma yin barazanar kisa ga wata mata da ta yi aiki a wani gidan tausa a shekarar 2021.

Idan har aka same shi da laifi, Sonko zai fuskanci zaman gidan yari na tsawon shekara 10 kuma za a hana shi tsayawa takarar shugaban kasa.

Ko da yake dai ya musanta tuhume-tuhumen da ake yi masa, yana mai cewa shiri ne da Shugaba Macky Sall ya yi na hana shi tsayawa takara a zaben shugaban kasa na 2024. Batun da Sall shi ma ya musanta.

Sonko bai kasance a gaban kotu ba a lokacin da aka fara shari’ar da misalin karfe 10: 00 agogon GMT amma wacce ta kai karar ta bayyana tare da lauyoyinta.

Mai shari’ar na gabatar da karar nan take ya dage zaman zuwa mako mai zuwa, biyo bayan muhawarar da barke tsakanin bangarorin biyu.

Lauyoyin Sonko sun bukaci karin lokaci don kara shiri la’akari da shari’ar ke da sarkakiya, yayin da lauyoyin wacce ta shigar da karar suka ki amincewa.

"Tun shekaru biyu da suka wuce muke shirye. Komai a shirye yake. Dole a yanke hukunci a yau, a kammala wannan shari’a," kamar yadda lauyan mai karar, El Hadj Diouf ya shaida wa kotun.

A baya-bayan nan ne dai aka yanke wa Sonko hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata shida a wata shari’ar batanci da ake yi masa, lamarin da ka iya hana shi tsayawa takarar shugabancin Senegal a shekarar 2024, sai dai idan ya samu nasara wajen daukaka kara kan hukuncin.

Zarge-zargen da ake yi wa Sonko sun sha haifar da tashin hankali da zanga-zangar da ba a saba gani ba a Senegal cikin shekaru biyun da suka gabata.

Dan siyasar dai ya samu karbuwa tare da samun goyon baya a tsakanin matasan kasar, wadanda ke cike da takaicin gwamnati mai ci, kuma suna ganin Shugaba Sall na kokarin sake darewa kan karagar mulki ne ta kowane hali

An jibge jami’an tsaro da dama a dukkan kewayen birnin Dakar a ranar Talata, rikicin ya kuma lafa bayan tarzomar ta ranar Litinin.

TRT World