Rikici ya barke a Dakar babban birnin Senegal bayan wata kotu ta yanke hukuncin daurin shekara biyu a kurkuku kan jagoran 'yan hamayyar kasar Ousmane Sonko bisa "gurbata zukatan matasa," abin da ke barazana ga aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Matasan da ke goyon bayansa sun rika jefa duwatsu kan 'yan sanda, yayin da su kuma suka mayar da martani da wurga musu barkonon-tsohuwa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum tara, a cewar Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar Antoine Felix Abdoulaye Diome, a jawabin da ya yi ta talabijin da safiyar Juma'a.
"Muna bakin cikin sanar da cewa rikicin ya yi sanadin lalata kayayyakin gwamnati da na daidakun jama'a, kuma abin takaici ya kai ga mutuwar mutum tara a birnin Dakar da Ziguinchor," in ji Diome.
Kakakin gwamnatin kasar Abdou Karim Fofana jami'ai sun tsaurara matakan tsaro a babban birnin kasar.
An toshe shafukan sada zumunta da dama daga yammacin Alhamis a Senegal — matakin da "zai yi tasiri sosai kan damar mutane ta sadarwa," a cewar wata kungiya mai suna NetBlocks da ke sanya ido kan harkokin intanet.
Sonko, babban mai hamayya da shugaban kasar Macky Sall, ba ya kotu lokacin da aka yanke masa hukunci ranar Alhamis. Bai halarci zaman kotun ba.
An yi amannar cewa yana gidansa da ke Dakar, wanda jami'an tsaro suka yi wa kawanya, bayan an hana shi fitowa a karshen mako.
Bayan an kwashe shekara biyu ana sa-in-sa tsakanin bangarorin biyu lamarin da ya jefa kasar cikin fargaba, yanzu ana iya tsare shi "ko wanne lokaci", a cewar Ministan Shari'ar Ismaila Madior Fall a hirarsa da 'yan jarida.
Jami'ar Dakar ta zama tamkar fagen yaki sakamakon wannan lamari.
Rikici ya barke tsakanin kungiyoyin dalibai matasa da 'yan sanda inda suka rika jifan jami'an tsaron da duwatsu. Su kuwa 'yan sandan sun rika wurga musu barkonon-tsohuwa.
An kona motocin bas da ke tsangayar koyar da aikin likita, da sashen koyar da tarihi da kuma sashen koyar da aikin jarida sannan aka kona ofisoshi. An rufe azuzuwa har sai abin da hali ya yi.
A wasu wuraren da ke wajen jami'ar, matasa sun kai hari a ofishin sayar da tikitin mota da sauran ofisoshin gwamnati a wasu bangarorin birnin, inda suka rika kona tayoyi da hana ababen hawa tafiya, a cewar wani dan jaridar AFP da ke daukar hotuna.
An rika watsa bidiyoyin rikicin a wasu sassan kasar a shafukan sada zumunta.
Rahotanni sun ce titunan Dakar aun zama tamkar kufayi bayan da mutane suka kulle kawunansu a cikin gidaje, babu abin da ake gani sai jami'an tsaro.
An bayar da rahoton aukuwar rikici a wasu bangarorin kasar irin su Casamance ida ke kudanci da Mbour da Kaolack da ke yammaci da kuma Saint-Louis da ke arewaci.