Ƙasashen Ethiopia da Somalia za su sake ganawa a mako mai zuwa a Ankara domin tattaunawa kan yarjejeniyar tashar ruwa ta Bahar Rum da Addis Ababa ta sanyawa hannu tare da yankin Somaliland da ya ɓalle, lamarin da ya haifar da takun-saka tsakanin ƙasashen makwabta na Gabashin Afirka.
Turkiyya ce ke shiga tsakani a ganawar da ƙasashen biyu suke yi domin tattauna saɓanin da ke tsakaninsu, kuma a watan jiya ta karɓi baƙuncin ministocin harkokin wajen Somalia da Ethiopia.
"An fara aiwatar da tsarin Ankara tsakanin Somalia da Habasha a karkashin jagorancin shugaban ƙasarmu. Mu ne muka assasa wannan tsarin da gagarumin ƙoƙari. A yanzu haka ƙoƙarin namu ya ci gaba, kuma muna shirin gudanar da ganawa ta biyu a makon gobe,” kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana a ranar Juma'a a taron manema labarai.
Sanarwar ta zo ne mako guda bayan Fidan ya ziyarci Addis Ababa inda ya gana da Firaministan Ethiopia Abiy Ahmed.
Batun tattalin arziki
Samun damar shiga Tekun Bahar Rum ya kasance wani muhimmin batu na tattalin arziki ga Ehiopia.
Amma yarjejeniyar da ta ƙulla a watan Janairu na ba da hayar wani fili mai nisan kilomita 20 a gaɓar tekun Somaliland don kafa sansanin sojojin ruwa ya janyo martani daga Somalia.
Somalia dai na ɗaukar Somaliland a matsayin wani yanki na ƙasarta, ta kuma yi tir da yarjejeniyar a matsayin cin zarafin 'yancin kanta da kuma yankinta.
Turkiyya dai na da daɗaɗɗiyar alaƙa da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu, kuma tana da ƙwarin gwiwa kan ƙoƙarin shiga tsakani na Ankara.