Rundunar sojojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe ‘yan bindiga 10 a jihar Katsina tare da kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar.
Ta bayyana haka ne ranar Alhamis a wata sanarwa da Kyaftin Ibrahim Yahaya, kakakin Rundunar Operation Hadarin Daji (OPHD ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa dakarun sojin sun kubutar da mutum tara, mata biyar da kananan yara hudu, da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su.
Rundunar ta ce an kubutar da mutanen ne a garuruwan Dansadau da Dandalla da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Sojojin sun ce ‘yan ta’adda da dama sun tsere dauke da harbe-harben bindiga a jikinsu.
“Ranar 3 ga watan Janairun 2024, Rundunar OPHD ta kaddamar da hare-hare a maboyar 'yan ta'adda a kananan hukumomin Batsari da Safana da ke Katsina, inda ta kashe 'yan ta'adda 10 yayin da wasu suka tsere dauke da harbe-haren bindiga a jikinsu," in ji sanarwar.
Rundunar ta ce ta kwace makamai da alburusai da babura da kuma wayoyin salula daga wurin ‘yan ta’addan.
Jihohin Katsina da Zamfara sun dade suna fama da matsalar masu garkuwa da mutane, wadanda ke zuwa gidaje da gonaki har ma da makarantu suna dauke mutane.
A lokuta da dama suna kashe su ko da an ba su kudin fansa.
Hukumomi sun sha alwashin kakkabe wadannan ‘yan bindiga, sai dai mazauna yankunan sun ce akwai bukatar kara kaimi wajen magance matsalar.