Sabon babban sifeton 'yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya ce yanzu jin sa yake kamar damisa da ta shirya "korar dukkan masu aikata laifuka" a kasar.
Ya bayyana haka ne bayan mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima, ya sanya masa anini na samun mukaminsa ranar Talata.
A ranar Litinin ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada sabbin hafsoshin tsaron Nijeriya, ciki har da Mr Egbetokun.
Nadin nasu na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da manyan kalubalen tsaro musamman na hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da gyauron 'yan Boko Haram da ma masu tayar da kayar baya na IPOB.
'Zaki'
Sai dai a yayin da yake jawabi ga 'yan jarida a Abuja jim kadan bayan an sanya masa sabon mukamin nasa, Mr Egbetokun ya ce ya matsu ya soma aiki ranar Laraba "domin a yanzu haka, zan gaya muku cewa ji na nake kamar damisa wadda ta shirya korar dukkan masu aikata laifuka a Nijeriya.
A wasu lokutan kuma ji nake kamar zaki da yake shirin cinye dukkan makiyan Nijeriya.”
Takaitaccen tarihin Mr Egbetokun
- Dan asalin jihar Ogun kuma an haife shi a watan Satumba na 1964
- Ya yi digirinsa na farko a fannin Lissafi a Jami'ar Lagos
- Ya yi digirinsa na biyu a Nazarin Injiniya da Gudanar da Kasuwanci a Jami'ar Lagos
- Ya soma aikin dan sanda a 1990
- Ya taba rike mukamin kwamishinan 'yan sanda na jihar Kwara
- Ya shugabanci sashen binciken manyan laifuka a hedikwatar 'yan sanda da ke Abuja