Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta yi kira ga 'yan tawayen M23 su ajiye makamansu. /Hoto: AP

Shugaban Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) zai gana da takwaransa na ƙasar Rwanda a wani taron gaggawa ranar Laraba, a yayin da 'yan tawayen M23 suke iƙirarin ƙwace muhimmin birnin Goma.

Majiyoyin tsaro sun ce ƙungiyar ta M23, wadda Rwanda ke mara wa baya, ta ƙwace filin jirgin saman Goma ranar Talata, bayan ta kwashe kwanaki da dama tana gumurzu da sojojin ƙasar, lamarin da ya kai ga kisan fiye da mutum 100 da jikkata kimanin mutum 1,000, a cewar wata ƙididdiga da kamfanin dillanacin labarai na AFP ya tattaro daga asibitoci.

Shugaban ƙasar DRC Felix Tshisekedi zai gana da takwaransa na Rwanda Paul Kagame ranar Laraba a wani "muhimmin" taro na Ƙungiyar Ƙasashen Gabashin Afirka da Kenya ke jagoranta, in ji shugaban ƙasar ta Kenya.

Har yanzu ba a san ɓangaren da ya fi iko da birnin na Goma ba, tsakanin dakarun ƙasar Kongo da 'yan tawayen M23, waɗanda suka yi iƙirarin ƙwace shi ranar Lahadin da ta gabata.

'Ajiye makamai'

A yayin da fafatawar ta lafa ranar Talata da daddare, babu abin da ake gani a kan tituna sai mayaƙan M23, a cewar masu aika rahotanni ga kamfanin dillancin labarai na AFP .

Majiyoyi a fannin tsaro sun ce "sojojin Kongo fiye da 1,200 sun yi saranda kuma an ajiye su" a sansanin MDD da ke filin jirgin saman DRC.

A yayin da Kwamitin Tsaro na MDD ya gudanar da taro ranar Talata a kan halin da ake ciki a Kongo, ya yi gargaɗi game yiwuwar sake fadawa cikin yaƙin ƙabilanci irin wanda a baya ya kai ga kisan kiyashi na 'yan ƙabilar Tutsi.

Bayan taron da aka yi ranar Lahadi, gwamnatin Kongo ta bayyana "mamaki" game da sanarwar da ba ta ɗora alhakin abin da ke faruwa a ƙasar kan Rwanda ba.

A wani taron gaggawa da ta gudanar ranar Talata, ƙungiyar Tarayyar Afirka ta yi kira ga mayaƙan M23 su "ajiye makamanku."

AFP