Shugaba Biya, wanda yake wa'adi na bakwai na shugabancin kasar, ya hau kan mulki a 1982 / Hoto: Reuters

Shugaban Kamaru Paul Biya, daya daga cikin wadanda suka fi dadewa a kan mulki a Afirka, ya yi sabbin nade-nade a Ma'aikatar Tsaron kasar, a cewar wasu bayanan soji da aka fitar a shafukan intanet.

Ya dauki matakin ne kwana guda bayan sojoji sun yi juyin muki a makwabciyarsu Gabon.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun ayyana Janar Brice Oligui Nguema a matsayin sabon shugaban kasar.

Sanarwar da Shugaba Biya ya wallafa a shafinsa na X wanda a baya ake kira Twitter ta ce an yi garambawul ga jami'in tsaron kasar.

Shugaba Biya, wanda yake wa'adi na bakwai na shugabancin kasar, ya hau kan mulki a 1982. A 2018 ya sake yin nasara a zaben da aka yi zargin an tafka magudi.

A gefe guda, Rwanda ta sanar da yin gagarumin garambawul ga jami'an tsaron kasar ranar Laraba lamarin da ya shafi manyan dakarun tsaron kasar.

Wata sanarwa da rundunar tsaron Rwanda ta fitar ta ce Shugaban kasar Paul Kagame ya "amince a yi ritaya ga gomman janar-janar, da manyan sojoji 83 da kuma kananan sojoji shida.”

Kazalika Kagame ya ya bayar da umarnin yin ritaya ga wasu manyan jami'an tsaro 86, a cewar sanarwar.

An yi wa sojoji akalla 678 ritaya bayan wa'adin aikinsu ya kare yayin da aka sallami wasu sojojin 160 saboda dalilai na rashin lafiya.

Sanarwar ta ce sojoji da dama da suka shiga yakin ceto Rwanda na 1994 da suka hada da Janar James Kabarebe, Janar Fred Ibingira da Lafanaar Janar Charles Kayonga na cikin wadanda aka yi wa ritaya.

A baya Janar Kabarebe da Janar Kayonga sun rike mukamin manyan hafsoshin tsaron rundunar sojin Rwanda a lokuta daban-daban.

Sauran wadanda aka yi wa ritaya su ne Laftanar Janar Frank Mushyo Kamanzi, jakadan Rwanda a Rasha da Manjo Janar Albert Murasira, tsohon ministan tsaron kasar.

Tun da farko a ranar ta Laraba, Kagame ya yi karin girma ga wasu matasan sojoji zuwa mukaman Kanar sannan ya nada wasu janar-janar don shugabantar wasu rundunonin soji.

A watan Yuni, Kagame ya nada Juvenal Marizamunda a matsayin ministan tsaro, inda ya maye gurbin Albert Murasira, wanda ke kan mukamin tun 2018.

TRT Afrika