Daga
Kudra Maliro
A wasu lokuta, sai wani mummunan abu ya faru ne kasa za ta fara daukar hanyar gyara. Ga Rwanda, babban abin da ya faru shi ne kisan-kiyashin shekarar 1994 wanda ya jawo babbar asarar rayuka a Afirka.
Shekara 30 bayan faruwar haka, yankin kasar na Great Rift Valley ya yi jagoranci wajen samar wa mata ci-gaba ta fuskar zamantakewar al'umma da siyasa da kuma kasuwanci.
Ta fuskar bai wa mata dama don shiga su yi harkokin shugabanci, Rwanda tana sahun gaba a wannan bangare a duniya, inda fiye da rabin mambobin majalisar dokokin kasar mata ne.
A yanzu mata na da fiye da kashi 61.3 cikin 100 na kujerun majalisar dokoki, ninki hudu na adadin mata da ake da shi a 1994, kuma hakan yana nufin adadin ya wuce tsaka-tsakin da ake bukata a duniya na kashi 26.4 cikin 100.
Ana kuma jinjina wa Rwanda kan yadda ta dukufa wajen yaki da cin zarafin mata, bayan bai wa mata damar zuwa makaranta.
Adadin mata da suka iya rubutu da karatu ya karu daga kaso 20 zuwa 91.7 cikin 100 a shekaru 20 da suka wuce. Kazalika adadin mata da suke kasuwanci ya nunka.
Damar da kasar ta samu ta karbar bakuncin babban taro kan Mata da 'Yan Mata wacce ita kasar Afirka da ta taba yin haka, an yi taron ne a birnin Kigali daga ranar 17 zuwa 20 ga watan Yuli, kuma taron manuniya ce kan yadda Rwanda take kokari wajen cimma manyan muradunta.
Kamar yadda gwamnatin kasar Rwanda ta bayyana taron wanda shi ne karo na hudu ya nuna yadda aka samu hadin kai da sadaukar da kai da kuma dukufa wajen samar da daidaiton jinsi.
Yawan halarta taron
Kimanin mutum 6,000 ne suka kai ziyara babban birnin Rwanda don halartar taron kwana hudu kan sararin samaniya mai taken "Space, Solidarity and Solutions".
Akwai kuma wasu mutum 2,000 da suka halarci taron intanet, Shugaba Paul Kagame ne ya kaddamar da taron a gaban shugabanni kamar Macky Sall na Senegal da Shugabar Ethiopia Sahle-Work Zewde da kuma Shugabar Hungary Katalin Novak.
"Tarihinmu a matsayin kasa ya nuna mana sauyi ba ya samuwa a dare daya. "Idan muka da hada kai, muka jajirce, muka kuma dukufa za su samu daidaito tsakanin maza da mata," in ji Shugaba Kagame.
Ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki da "su ci gaba da yin aiki tare cikin hanzari don gina al'umma mai adalci kuma wadda za ta yi nasara".
Daga bangarenta, gwamnatin Rwanda ta yi aiki da maganganun da ta yi tsawon shekaru 30 da suka wuce, inda ta kirkiro tsare-tsare don taimaka wajen damawa da mata a fannin tattalin arziki da rayuwar al'umma.
Mireille Batamuliza, babban sakatare a ma'aikatar jinsi da bunkasa rayuwar iyali, ya yi amannar cewa dufuka wajen aikace-aikacen ne ya kawo sauyin.
"Ta hanyar shirya wannan taron duniyar, duniya ta mayar da hankali kan Rwanda. Mun tattauna kan kokarin da Rwanda ke yi wajen samar da daidaiton jinsi.
Kuma wata dama ce ta nuna yadda kasarmu ta samu ci gaba, da kuma bayar da tabbacin cewa akwai yiwuwar samun sauyi ta hanyar samar da daidaiton jinsi da kuma karfafawa mata gwiwa," kamar yadda Mireille Batamuliza, babban sakatare a ma'aikatar jinsi da samar sa daidaiton Italian, ya shaida wa TRT Afrika.
"Tun da farko shugabanci mai hangen nesa ya sa an samar da kundin tsarin mulki da ya tabbatar da warewa mata kaso 30 cikin 100 na kujeru a hukumomin gwamnati.
Kuma akwai hukumomi da ke sanya ido don tabbatar da ana bin wannan tanadi na tsarin mulki," in ji shi.
Samar da daidaito a al'umma
Dokta Jeannette Bayisenge, Rwanda ministar jinsi da bunkasa rayuwar iyali, ta yi amannar cewa mummunan tarihin kasar wato kisan kiyashin shekarar 1994, ya kasance abin da ya zaburar da kasar wajen bunkasa samar da daidaiton jinsi.
"Kisan-kiyashin Tutsi ya bar babban taro a al'ummarmu," in ji Bayisenge. "Tun daga lokacin, mata suke ganin ba a ba su dama ba kafin shekarar 1994 sun samu mukamai da matsayi a al'umma.
Wannan sai ya zama wani abu da zai taimaka wa Rwanda wajen shawo kan kalubalen da suka biyo bayan kisan kiyashin."
Kamar yadda Dokta Bayisenge, wanda kuma malami ne fanni nazari kan jinsi a Jami'ar Rwanda ya ce babban nasarar da aka samu wajen sake gina kasar shi ne "fahimtar da aka yi cewa idan ana so a kawo gagarumin ci gaba, to yana da muhimmanci a samu gudunmuwar mata kuma a ba su dama da za su taimaka wajen kawowa kasar ci gaba."
A yau, mata a Rwanda sun samu matsayi a gwamnati da fannin kasuwanci da shugabanci da kuma wasu muhimman fannonin tattalin arziki.
"Kokarin da muke wajen samar da daidaiton jinsi yana nan daram, kuma za mu ci gaba da aiki kan makoma inda kowane dan Rwanda zai samu dama daidai da kowa da kuma yadda zai taimaka wajen ci gaban kasar," in ji Dokta Bayisenge.
Da shirin Women Deliver, muradan Rwanda na karfafa gwiwa da aiwatar da tsare-tsaren na shekaru masu zuwa za su iya zama wani abin koyi ga sauran kasashen duniya.