An gano mace-macen jarirai  310 a shekarar 2017 cikin jarirai 100,000 da aka haifa a Ghana /Hoto: GNA / Photo: Reuters

Wani bincike da aka gudanar kan tsangwamar da ake yi wa mata masu juna biyu a kasar Ghana ya gano cewa mata biyu cikin uku suna fuskantar wulakanci ko cin zarafi a hannun ma'aikatan jinya a lokacin nakuda da kuma haihuwa.

Wata 'yar Ghana wacce ke zaune a kasar Jamus, Dokta Abena Yalley ce ta jagoranci binciken kuma ita da tawagarta sun tattauna da mata 2,142 tsakanin watan Satumbar 2021 zuwa watan Fabrairun 2022 dangane da wulakanci ko cin zarafin da ake yi musu yayin da suke dauke da juna biyu a yankin Yammacin kasar da kuma yankin Ashanti, a cewar kamfanin dillancin labaran Ghana.

An yi wa binciken taken: "Humanizing the Birthing Process" kuma ya yi nazari ne kan abubuwan ke jawo mutuwar mata da jarirai da bambancin adadin matan da ke zuwa awon ciki amma kuma ba sa zuwa asibiti lokacin haihuwa abin da ke jawo matsalar mace-macen mata da jarirai yayin haihuwa.

Binciken ya gano cewa an samu mace-mace 310 a shekarar 2017 cikin jarirai 100,000 da aka haifa, wanda hakan ya zama cikas ga cimma Muradu Masu Dorewa na Majalisar Dinkin Duniya (SDGs).

Dokta Abena Yalley ta shirya taro inda ta gana da nas-nas da ungozoma da kungiyoyin mata da sauransu, kuma ta bukaci a dauki mataki cikin gaggawa dangane da cin zarafi ko wulakanta mata masu juna biyu a Ghana.

"Cin zarafin mata masu ciki a asibitoci ya hada da wulakanci da rashin tausayi da rashin mutunta mai juya biyu da kin ba su kulawa da zagi da sauransu," in ji ta.

Binciken ya gano cewa ana yi wa masu juya biyu ihu da fada da kuma duka, sai kuma kin yi musu allurar kashe zafi yayin da ake musu dinki a jiki wadanda dabi'u ne marasa kyau da ake samu a asibitoci.

Bincike ya ce mata marasa miji da 'yan mata da suka dauki ciki ne suka fi kuskantar wannan matsala.

Kamar yadda binciken ya bayyana abin ya jawo mata da yawa sun gwammace su haihu a gida maimakon haihuwa a asibiti a hannun kwararrun ma'aikatan jinya.

Matan da suka fuskanci wannan matsalar, abin ya kan shafi tunaninsu kuma ya kan sanya musu tsoron zuwa asibiti. Abin da binciken ya ce zai jawo cikas ga nasarar da aka samu wajen raguwar mace-macen mata da jarirai da yaduwar cutar kanjamau tsakanin uwa zuwa jaririnta

A karshe binciken ya ce dole ne a sake fasalin manhajar karatu a makarantun koyon aikin jinya ta yadda za a cusa wa dalibai tausayi a zukatansu da kuma samar tsarin shigar da korafi a asibitoci.

TRT Afrika da abokan hulda