Hukumomi sun ce akwai mutum 11 wadanda ake zargin suna dauke da cutar. Hoto/CDC

Akalla mutum guda ya rasa ransa sakamakon cutar anthrax da ta bulla a gundumar Binduri da ke yankin Upper East na Ghana.

Kafar watsa labarai ta kasar Ghana ta ruwaito cewa mutumin ya mutu bayan cin mushen wata saniya wadda ta mutu sakamakon cutar ta anthrax.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta yankin Upper East ta bayyana cewa akalla shanu hudu suka mutu sakamakon cutar ta anthrax a Binduri.

Daraktan kiwon lafiya na ma’aikatar Emmanuel Dzotse, ya ce tuni jami’ansa suka soma bin diddikin wasu mutum 11 wadanda ake zargin sun ci naman shanun da suka kamu da cutar.

Dakta Dzotse ya kuma gargadi duka gundumomin da ke makwaftaka da Binduri da su zama a ankare tare da kara sa ido domin kauce wa yaduwar wannan cuta.

Ya kuma tabbatar da cewa za a yi gwaji ga duka wadanda ake zargin sun kamu da cutar kuma za a yi musu magani da Ciprofloxacin da kuma Doxycycline.

Dakta Dzotse ya kuma jaddada cewa jami’ansa za su dukufa wajen wayar da kai kan cutar da kuma yadda za a iya kiyaye yaduwarta, haka kuma ya bukaci jama’a da su guji cin matattun shanu ba tare da bincike kan musabbabin mutuwarsu ba.

Ya kuma kara jawo hankalin makiyaya da sauran masu kiwon shanu a duka gundumomin da su rinka hulda da likitocin dabbobi domin kiyaye wannan cuta

TRT Afrika da abokan hulda