Hukumar da ke yaki da safarar miyagun kwayoyi ta Ghana, Nacoc, ta ce ta kama dauri 54 na ganyen tabar wiwi da nauyinsu ya kai kilo 12.67.
Hukumar ta ce ta kama wadannan kayayyaki ne a ranar Laraba 23 ga watan Mayu a filin jirgin sama na Kotoka da ke Accra babban birnin kasar.
A sanarwar da ta fitar a shafukanta na sada zumunta a ranar Juma’a, hukumar ta ce an boye daurin wiwin ne a cikin wani mutum-mutumi na katako wanda aka yi niyyar kai shi Birtaniya.
Jami’an hukumar na Nacoc a yayin duba kayayyaki da na’ura suka gano wiwin a cikin mutum-mutumin wadda aka kiyasta kudin tabar kan dala 127,713.6.7.
Hukumar ta ce za ta ci gaba da bincike da kuma bin diddiki domin tabbatar da cewa an dauki mataki kan masu safarar tabar.
Ko a kwanakin baya sai da hukumar ta Nacoc ta kama hodar ibilis a filin jirgin na Kotoka da ta kai ta dala 300,000