Ministan tsaron Ghana da jakadan China a Ghana ne suka kaddamar da ayyukan gine-ginen da China take yi wa sojin Ghana/Hoto: Ghana Armed Forces

Kasar China za ta yi wa sojin Ghana gine-gine tara a fadin kasar da ke yammacin Afirka.

Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ruwaito cewar gine-ginen na cikin tallafin sojin da kasar China ke yi wa kasar don inganta kayayyakin sojin Ghana.

Kamfanin dillancin labaran Ghanan ya ce kamfanin gina jiragen kasa na China ne zai yi gine-ginen a sansanonin da makarantun sojin Ghana da ke Shai Hills da Nutekpor-Sogakope da Takoradi da Bundase da ke kusa da Tema.

Ministan tsaron Ghana, Mista Dominic Nitiwul, ya ce aikin ya zo ne a lokacin da sojin Ghana ke bukatar magance matsalar rashin gine-gine da sojin kasar ke fuskanta.

Ministan ya yaba wa jakadan China a Ghana, Mista Lu Kun, da sojojin China da duk wadanda suka sanya hannu wajen tabbatar da cewa an fara ayyukan.

A nasa bangaren, jakadan China a Ghana ya ce Ghana ce kasa ta biyu a Afirka wadda huldarta ta diflomasiyya da China ke ci gaba da habaka.

Labarin dai bai bayyana ko kyauta China ke yi wa sojin Ghanan ba ko kuma bashi ne.

Kasashen yammacin duniya sun dade suna nuna fargaba game da karin karfin China a nahiyar Afirka, lamarin da suke yi wa lakabi da “tarkon bashi”.

Ghana ta kasa ci gaba da biyan basussakan da ake binta a shekarar da ta gabata.

Lamarin da ya sa ta sake komawa gun masu bin ta bashin don ta sake tsara basussukan da ake bin ta ta yadda za ta iya ci gaba da biyansu.

Shugaban Ghana ya ce rancen da gwamnatin kasar ke jira daga asusun lamuni na IMF ba zai sauya yanyin kasar nan take ba/Hoto:Facebook/Nana Akufo-Addo

Kuma a halin yanzu kasar tana dakon rancen dala biliyan uku daga asusun ba da lamuni na IMF.

TRT Afrika da abokan hulda