Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya bayyana aniyyarsa a karon farko ta sake tsayawa takara karo na hudu a babban zaben kasar da za a gudanar a shekara mai zuwa.
"Tabbas, ni dan takara ne," a cewar Kagame, wanda ya shafe sama da shekaru 20 yana mulkin kasar Ruwanda, a hirar da mujallar Faransa Jeune Afrique ta yi da shi wadda ta wallafa a intanet ranar Talata.
"Na gamsu da aminci da 'yan Ruwanda suka ba ni. Zan yi musu hidima yadda ya kamata," a cewar shugaban mai shekaru 65.
A watan Maris ne gwamnatin Ruwanda ta yanke shawarar daidaita ranakun gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki da zaben shugaban kasa, wanda za a gudanar a cikin watan Agustan shekara mai zuwa.
Ko da yake a baya Kagame bai fito fili ya bayyana aniyarsa ba, amma ya jagoranci gyaran kundin tsarin mulkin kasar da ke cike da ce-ce-ku-ce da ya ba shi damar yin wa'adi na uku.
A shekarar 2017 ne ya lashe zabe karo na uku, inda ya samu kusan kashi 99 cikin 100 na kuri'un da aka kada.