Gwamnatin Ghana ta karrama fiye da ma'aikatan lafiya 300 da suka yi yaki da cutar korona a kasar.
Shirin bayar da lambar yabo, wanda shugaban Ghana Nana Akufo-Ado ya kaddamar, wani yunkuri ne na yaba wa ma’aikatan kiwon lafiya kan gagarumar gudunmawar da suka bayar lokacin da cutar COVID-19 ta barke a kasar.
Kamfanin dillanci labaran na Ghana News Agency ya rawaito cewa sama da ma’aikatan lafiya 300 daga babban asibitin koyarwa na Tamale ne suka samu wannan lambar yabo ta shugaban kasa ranar Talata.
Daga cikin ma’aikatan da aka karrama akwai likitoci da nas-nas da ungozoma da masu hada magunguna da jami’an abinci mai gina jiki da ma’aikatan dakin gwaje-gwaje da direbobi da kuma masu aikin wanki na asibitin da masu gyaran wutar lantarki da dai sauransu.
An mika su takardar karramawar ce mai dauke da shaidar sa hannun shugaban kasar Akuffo-Addo.
Kazalika an ba da lambar yabo ga babban asibitin TTH a matsayin wurin da ya nuna juriya da kwazon aiki wajen samar da yanayin da ya dace a lokacin barkewar cutar.
Bikin ba da kyautar na daga cikin jerin abubuwan alherin da shugaban kasar ya kuduri aniyar yi a farkon wannan shekara ga mutanen da suka gudanar da aikinsu cikin hazaka a bangarori daban-daban a kasar.
Bikin, wanda aka gudanar a Accra, ya zakulo ma’aikata da ke kan gaba a dukkan ma’aikatu daga sassan kasar tare da jinjina musu da kuma karrama su.
Ministan arewancin yankin kasar, Allhaji Shani Alhassan Shaibu wanda ya wakilci shugaban Akufo Ado a bikin, ya ce takardar shaidar karramawar wata alama ce ta nuna nasara a rayuwa.
''Tasirin lambar yabon ya wuce rubutu a takarda kawai, ya kamata mutanen da aka bai wa lambobin yabon su dauki kansu a matsayin wadanda suka samu dama da ba kasafai ake samu ba,'' kamar yadda ya shaida wa Ghana News Agency .