Shugaban Kenya William Ruto ya bayyana zanga-zangar da aka yi ranar Talata da ta janyo mutuwar mutum biyar da jikkata fiye da mutum 90 a matsayin ‘cin amanar kasa.’
A wani jawabi da ya yi wa ‘yan ƙasa ranar Talata da daddare, Ruto ya ce gwamnati za ta ƙaddamar da martani na gaggawa da zai hukunta “waɗanda suka shirya, da waɗanda suka ɗauki nauyi da masu iza wuta da duk masu hannu a tashin hankali da taɓarɓarewar al’amura.”
‘Yan Kenya daga sassan ƙasar da dama da suka haɗa da babban birnin ƙasar Nairobi, sun yi arangama da ‘yan sanda tsawon yini guda, suna zanga-zangar adawa da ƙarin harajin da suka yi kukan cewa ya yi “yawa” kuma “na rashin imani" ne.
Shugaba Ruto yana so ya fito da sabbin haraji kan audugar ƙunzugu ta mata da ake shigar da ita daga waje da wayoyin hannu da babura da kuma sanya haraji kan filayen da aka ware su da sunan wasu tsare-tsare na iyali.
Kasafin kuɗin da ba a taɓa yin irinsa ba
Ruto, wanda ya tsara ƙasafin kuɗin da ya fi duk na baya yawa na kuɗin Kenya shilling tiriliyan 3.9 – ko dala biliyan 30 – na shekarar 2024/2025, ya ce Kenya na buƙatar ƙarin kuɗaɗe, don kauce wa dogaro kan ciyo bashi.
Gwamnati ta tura sojoji domin taimaka wa ‘yan sanda domin kawo ƙarshen zanga-zangar.