Shugaba Ramaphosa ya ce suna fatan za su warware rikicin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine. Hoto/Getty

Shugabannin Afirka sun isa Turai domin yin sulhu a rikicin da ke faruwa tsakanin Rasha da Ukraine.

Su ne na baya bayan nan da suke yunkurin yin sulhu a yakin da aka soma a watan Fabrairun bara wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

A sanarwar da ya fitar ranar Alhamis da almuru, shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce suna kan hanyarsu ta zuwa Turai domin bayar da gudunmawar ''Afirka ta neman zaman lafiya da magance rikici tsakanin Ukraine da Rasha.''

Sauran kasashen da ke cikin wannan tawaga su ne, Zambia, Comoros, Kongo Brazzaville, Masar, Senegal da Uganda.

Sai dai shugabannin kasashen Uganda da Masar da Comoros sun aike da wakilai ne.

Tun da farko shugaban Afirka ta Kudu Ramaphosa ya isa Poland tare da sauran shugabannin kuma ya ce ''yanzu muna kan hanyarmu ta zuwa babban birnin Ukraine Kyiv don tattaunawa'' da Shugaba Volodymyr Zelenskyy ranar Juma'a.

Daga nan tawagar za ta isa St Petersburg da ke Rasha, inda za su "tattauna da Shugaba Putin ranar Asabar."

Shugaban Senegal Macky Sall ya ce ba sa jin dadin rikicin da ke faruwa tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa: “Ba ma so a alakanta mu da wannan rikici. A bayyane take cewa muna kaunar zaman lafiya . . .wannan ita ce matsayar Afirka.”

TRT Afrika