Shugaba Ramaphosa ya ce yakin Rasha da Ukraine yana mummunan tasiri kan kasashen Afirka./Hoto:Getty

Shugabannin kasashen Afirka da ke neman yin sulhu tsakanin Rasha da Ukraine ta shaida wa Shugaba Vladimir Putin cewa lokaci ya yi da za a kawo karshen yakin da kasashen ke yi.

Sun bayyana hakan ne ranar Asabar a yayin ziyarar da suka kai kasar ta Rasha suna masu cewa yakin yana yin illa ga Afirka da ma daukacin duniya.

Tawagar ta kunshi shugabannin kasashen Senegal, Macky Sall; Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa; Zambia, Hakainde Hichilema; Comoros, Azali Assoumani, wanda shi ne shugaban Tarayyar Afirka; da kuma firaiministan Masar.

"Mun zo nan ne domin mu mika sako karara cewa ya kamata a kawo karshen wannan yakin... dole ne a yi sulhu ta hanyar diflomasiyya," in ji Shugaba Cyril Ramaphosa, a taron manema labaran da suka gabatar a St Petersburg.

A nasa bangaren, Shugaba Putin ya yi "maraba da sigar Afirka ta adalci" a wannan rikici yana mai cewa "kofarmu a bude take mu yi tattaunawa mai ma'ana tare da dukkan wadanda suke son wanzar da zaman lafiya bisa adalci da mutunta juna."

Tun da fari tawagar shugabannin Afirka ta gana da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ranar Juma'a domin yin sulhu tsakaninsa sa takwaransa na Rasha.

Shugaba Zelensky ya gayyaci shugabannin Afirka su halarci "taron kasashen duniya na samar da zaman lafiya" inda zai gabatar da "tsarin zaman lafiya."

Shugabannin Afirka su ne na baya bayan nan da ke yunkurin yin sulhu a yakin da aka soma a watan Fabrairun bara wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

TRT Afrika da abokan hulda