Dama daya daga cikin manyan ayyukan da Hisba ta saba gudanarwa shi ne auren Zawarawa a fadin jihar. Hoto: Daurawa Facebook

Sabon Kwamandan Hisba na Kano da ke arewacin Nijeriya Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shiga ofis a karo na uku, bayan sake nada shi a mukamin da gwamnan Jihar Abba Kabiru Yusuf ya yi a ranar Litinin.

Sheikh Daurawa ya shugabanci Hukumar Hisba ta Kano sau biyu a jere a lokutan mulkin Gwamna Rabi'u Kwankwaso da Abdullahi Ganduje.

A yayin jawabin da Babban kwamandan na Hukumar Hisba ya gabatar a harabar hukumar kafin shiga ofis don fara aiki a ranar Laraba, ya yi godiya ga Ubangiji sannan ya neman hadin kan abokan aikinsa ‘yan Hisba da sauran ma’aikatan hukumar.

Cikin muhimman abubuwan da Sheikh Daura ya ce zai mayar da hankali a kai a lokacin mulkin nasa, har da batun auren zawarawa.

Matakan Auren Zawarawa

Dama daya daga cikin manyan ayyukan da Hisba ta saba gudanarwa shi ne auren Zawarawa a fadin jihar.

Malam Daurawa ya bayyana cewar tuni gwamnan Kano Abba Gida-Gida ya bayar da umarnin a tantance mata da maza 2,000, wato mata dubu daya da maza dubu daya don a aurar da su bisa tallafin gwamnatin jiha.

Wannan shi ne fom din auren zawarawa a Jihar Kano. Hoto: OTHERS

Daurawa ya bayyana matakan da za a bi wajen tantancewa da zabo wadanda za su amfana da shirin auren kamar haka bayan kafa kwamitoci biyar:

  • Za a raba fom a dukkan kananan hukumomi

Babban Kwamandan na Hisba ya bayyana za a fara shirin auren ne da raba fom fom a kananan Hukumomin Kani 44. Kowacce karamar Hukuma za a ba ta fom guda 20.

Za a raba wa duk masu sha'awar auren don su cike tare da mika wa Hukumar.

Zai zama jumullar 880 kenan a kananan hukumomi 44, sai sauran 120 da za a rabar daga hedikwatar Hukumar da ke birnin Kano.

  • Tantancewa

Bayan an dawo da fom da aka cike, sai kuma a zo a tantance a ga ko mutum ya cancanta ko bai cancanta ba don shiga shirin.

Wadanda aka tantance aka tabbatar sun cika sharuddan da aka bayyana, sai a mika su ga hukumar ta Hisba.

  • Shiryawa angwaye da amare bita

Bayan an tantance, za a shirya wa ma'auratan bita, za a ilimantar a su, a wayar musu da kai a kan mene ne aure, yaya ake zaman aure, mene ne hakkokin ma'aurata a kan juna da dai sauran su.

  • Tantance lafiya

Bayan an shiryawa masu shirin angwancewa bita, Hukumar Hisba za ta hada kai da Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano don tantance lafiyar wadanda za su yi auren.

Malam Daurawa ya ce, za a yi wa ma'auratan gwajin kwayar cutar HIV da ciwon sanyida na nau'in jini da ciwon hanta da ta'ammali da miyagun kwayoyi da kuma na juna biyu.

Babbar manufar hakan ita ce don a tabbatar da lafiya da ingancin kowa, ta yadda wani ba zai cutar da wani ba.

Babban malamin ya jaddada cewar sai mutum mai cikakken hankali, wanda aka san asalinsa, mai sana'a da sanin ya kamata za a aurawa mace.

Umarni da kyakkyawa da hani da aikata mummuna

Sheikh Daurawa ya bayyana cewa babban aikin Hisba shi ne Umarni da kyakkawan aiki da hani da mummuna, kamar yadda Allah Madaukakin Sarki Ya ba da umarni a ayoyi da dama na Kur'ani Mai Tsarki da kuma yadda Annabin Tsira ya yi umarni kuma aka gani a Hadisai.

Sheikh Daurawa ya jaddada cewa dole ne a samu wani bangare na al’umma da zai dinga umarni da kyakkyawa da hani da mummuna kuma za a ci gaba da wannan aiki a dukkan fadin jihar Kano.

Shugabanci bisa adalci

Sabon Kwamandan na Hisba ya bayyana cewa zai gudanar da jagorancin hukumar bisa adalci ba tare da karbar gulmace-gulmace ba.

Malam Daurawa ya ce “Kun san ba na son gulma, duk wanda ya kawo min gulmar wani to zan kira wancan, na ce ya maimaita abun da ya fada a gabansa ya ji.”

Aiki tare da kowanne Dan Hisba

Malam Daurawa ya nemi hadin kan dukkan ma’aikatan Hisbah domin samun nasarar gudanar da ayyukansu. Ya ce idan ya samu nasara, to nasararsu ce gaba daya, a saboda haka dole ne kowa ya bayar da gudunmowa da hadin kan nasarar wannan aiki da nauyin da aka dora musu.

Aiki bisa dokokin da aka kafa Hukumar Hisba a kansu

Sabon kwamandan na Hisbah ya kuma bayyana cewa dukumar na da dokoki da iyakoki. Za su gudanar da ayyukansu bisa wadannan dokoki ba tare da keta haddi ba.

Dakarun Hisba sun gudanar da faretin tarbar sabon kwamandan nasu cikin annushuwa da walwala.

TRT Afrika