Hoto/KNSG

Hukumar kula da tsara birane ta jihar Kano ta gudanar da wani gagarumin rusau a jihar.

A wata sanarwa da sakataren watsa labaran jihar Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya fitar a ranar Asabar, ya tabbatar da rusa gine-ginen da ke jikin katangar filin sukuwa na jihar da ke unguwar Nasarawa.

Tun da sanyin safiyar Asabar kafofin watsa labaran jihar suka soma ruwaito batun rusau din tare da cewa gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da kansa ya jagoranci gudanar da rusau din da misalin karfe biyu na dare.

Hoto/Salisu Yahaya Hotoro

Sanarwar gwamnatin Kano ta ce rusau din da ta yi yana daga cikin alkawuran da ta dauka na yakin neman zabe inda ta ce za ta rusa wuraren da aka gina ba bisa ka’ida ba a makarantu da masallatai da wuraren wasan yara da makabartu da asibitoci.

Wannan rusau din na zuwa ne kasa da mako guda bayan sabon gwamnan ya hau kan karagar mulki.

Tun a baya sabon gwamnan ya sha alwashin waiwayar gine-ginen da aka yi da kuma wuraren da aka siyar ba bisa ka’ida ba a jihar.

Kafafen watsa labarai na jihar da kuma shafukan da ke da alaka da gwamnatin Kano na Kwankwasiyya sun wallafa hotuna da dama na gine-ginen da aka rusa.

TRT Afrika da abokan hulda