Hukumomi sun zargi Binance, wanda shi ne kamfanin kirifto mafi girma a duniya da janyo karyewar darajar kuɗin ƙasar. / Hoto: AA

Nijeriya ta shigar da ƙara a kotu tana neman a tilasta wa kamfanin hada-hadar kuɗin kifito Binance ya biya dala biliyan 79.5 saboda asarar da kamfanin ya janyo wa ƙasar a fannin tattalin arziki, sakamakon hada-hada da ya yi a ƙasar, da kuma dala biliyan biyu na bashin harajin da ake bin kamfain, kamar yadda takardun kotu suka nuna a ranar Laraba.

Hukumomi sun zargi Binance, wanda shi ne kamfanin kirifto mafi girma a duniya da janyo karyewar darajar kuɗin ƙasar, kuma sun tsare biyu daga manyan jagororin kamfanin a 2024, bayan shafukan intanet na kamfanonin kirifto sun saka kuɗin Nijeriya naira a matsayin kuɗin da za a iya hada-hada da shi a shafukan.

Bininace, wanda bai yi rijista ba a Nijeriya ba, bai mayar da martani nan take kan buƙatar ji daga gare shi ba. A baya dai ya ce yana aiki tare da Hukumar Tattara Haraji ta NIjeriya FIRS don warware batun bashin harajin da ake bin sa.

A takardun da Reuters ta gani, hukukmar ta FIRS ta yi zargin cewa Binance yayi “harkokin kuɗaɗe sosai” a Nijeriya, don haka dole ne ya biya harajin da kamfanoni suke biya kan kuɗaɗen da suka samu. FIRS na neman kotu ta bayyana cewa Binance zai biya harajin shekarun 2022 da 2023, da kuma 10% a kan kuɗin kowace shekara na harajin da da bai biya ba.

Zargin ƙin biyan haraji

FIRS tana kuma neman 26.75% na kuɗin ruwa kan kuɗaɗen harajin da ba a biya ba, kamar yadda yake a farashin bashi daga Babban Bankin Ƙasar CBN.

Dama dai Binance na fuskantar tuhume-tuhume huɗu na ƙin biyan haraji, bayan matakin da gwamnati ta ɗauka a kansa a bara.

Tuhume-tuhumen sun haɗa da rashin biyan harajin da ake biya kan kayayyakin da aka saya, wato VAT, da harajin da kamfanoni suke biya, da rashin bayar da bayanan haraji, da kuma haɗa baki da abokan hulɗarsa wajen kauce wa biyan haraji ta hanyar amfani da manhajarsa.

Binance, wanda yake ƙalubalantar tuhume-tuhumen, ya sanar a watan Mayun bara cewa ya dakatar da duk wata hada-hada da cinikayya da naira.

Kamfanin yana kuma fuskantar wata wata tuhumar daban ta fitar da kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya, wacce Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa EFCC ke yi masa, zargin da Binance ɗin ya musanta.

TRT Afrika