Hukumar tsaro ta DSS a Nijeriya ta ce Godwin Emefiele, shugaban babban bankin kasar da aka dakatar daga aiki, yana hannunta.
Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ranar Asabar da rana ta tabbatar da cewa "Mr Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Nijeriya (CBN) da aka dakatar, yanzu yana hannunmu domin gudanar da bincike."
Sanarwar, wacce kakakin DSS, Peter Afunanya, ya sanya wa hannu ta kara da cewa "muna jan hankalin al'umma, musamman 'yan jarida su yi taka-tsantsan wajen bayar da rahoto game da wannan batu."
Tun da farko a safiyar Asabar, DSS ta musanta cewa babban jami'in bankin kasar yana hannunta.
A ranar Juma'a da maraice ne shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya dakatar da shugaban Babban Bankin Kasar Godwin Emefiele nan take.
Wata sanarwa da Willie Bassey, daraktan sadarwa a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar, ta ce an dakatar da shugaban Babban Bankin Nijeriya ne bayan an gudanar da bincike a kan ofishinsa da kuma yadda ya tafiyar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki.
An umarce shi ya mika ragamar tafiyar da bankin a hannun mataimakinsa Mr. Folashodun Adebisi Shonubi.
Godwin Emefiele ya aiwatar da sauye-sauyen da suka jawo ce-ce-ku-ce a fannin tattalin arzikin Nijeriya.
A watan Oktoban 2022, ya sauya fasalin takardun naira 200, 500 da kuma 1,000 da zummar rage hauhawar farashin kayayyaki da yin kudin-jabu da kuma biyan kudi ga masu garkuwa da mutane.
Sai dai matakin ya jefa 'yan kasar cikin mawuyancin hali sannan 'yan siyasa sun bayyana cewa an fito da shi ne da zummar cin zarafinsu.
An nada Emefiele a matsayin shugaban Babban Bankin Nijeriya a 2014 bayan an dakatar da Sanusi Lamido Sanusi.