EFCC ta kama mutum 70 bisa zargin zamba da sojan gona a jihohi hudu na Nijeriya

EFCC ta kama mutum 70 bisa zargin zamba da sojan gona a jihohi hudu na Nijeriya

Hukumar ta ce ta kama mutanen ne a jihohin Kaduna da Sokoto da Cross River da kuma Oyo.
Hukumar ta ce za a gurfanar da su a kotu ba tare da bata lokaci ba /Hoto: EFCC

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa, EFCC ta ce ta kama mutum 70 daga jihohi daban-daban na kasar bisa zargin su da aikata laifukan zamba da sojan gona.

EFCC ta wallafa wadannan kame ne a shafinta na Twitter ranar Alhamis.

Hukumar ta ce ta kama mutanen ne a jihohin Kaduna da Sokoto da Cross River da kuma Oyo.

Mutum 28 a Jihar Cross River

EFCC ta kama mutum 28 a birnin Calabar na Jihar Cross River na kudu maso kudancin kasar, ciki har da wasu tagwaye maza, bisa zargin su da zamba ta intanet.

Binciken farko-farko ya nuna cewa wasu daga cikin masu laifin sun kware a damfara da sunan soyayya yayin da wasu kuma suke kware wajen yin sojan gona don yin zamba.

Cikin kayayyakin da hukumar ta kwace daga hannun wadanda ake zargin sun hada da wayoyi da komfutoci da mota biyar da manhajar hada intanet.

Hukumar ta ce za a gurfanar da su a kotu ba tare da bata lokaci ba.

Mutum uku a Jihar Sokoto

A Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Nijeriya kuwa Mai Shari’a Muhammad Sifawa na Babbar Kotun Jihar ne ya yanke wa wasu mutum uku hukuncin daurin shekara hudu ga kowannen su, bisa samun su da laifin damfara.

Cikin kayayyakin da EFCC ta kwato har da motoci na alfarma bakwai /Hoto: EFCC

EFCC ce ta kama su ta kuma gurfanar da su a gaban kotun kan tuhumar su da laifin yin sojan gona a matsayin su baki ne ‘yan kasashen waje, inda suka dinga damfarar mutane.

Mutum biyu a Jihar Kaduna

Hukumar EFCC ta ce a Jihar Kaduna ta arewa maso yammacin Nijeriya kuwa ta samu nasara a kotun da ta gabatar da wasu mutum biyu bisa zargin su da zambar intanet, inda aka yanke musu hukuncin daurin shekara uku a gidan kaso.

Bincike ya nuna yadda wadannan mutane suka dinga amfani da shafukan soshiyal midiya wajen zambatar mutane.

Mutum 37 a Jihar Oyo

A can birnin Ibadan da ke Jihar Oyo a kudu maso yammacin Nijeriya kuwa mutum 37 EFCC ta kama kan zargin su da zambar intanet.

Hukumar ta ce an kama su ne a Rukunin Gidaje na Ologolo da Omi-ado.

Sannan an kwato wasu kayayyaki a wajen su da suka hada da motoci na alfarma bakwai da babur daya da wayoyi da komfutotci da sauran abubuwa.

Za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike in ji EFCC.

TRT Afrika da abokan hulda