Nijeriya ta gargaɗi 'yan ƙasarta da ke shirin tafiya Birtaniya bayan wata tarzoma ta adawa da bayar da mafaka ta ɓarke a Birtaniyar.
An kashe wasu mata matasa uku inda wasu yara biyar suka samu mummunan rauni a yayin wani harin wuƙa a lokacin da suka halarci wurin koyon rawa na Taylor Swift a ranar Litinin 29 ga watan Yuli.
Tarzoma ta ɓarke a garuruwa da birane da ke faɗin ƙasar, inda masu zanga-zanga dangane da adawa da baƙi masu shiga ƙasar suka yi fito-na-fito da 'yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Musulmi a wasu lokutan.
"Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fitar da sanarwa dangane da 'yan Nijeriya da ke shirin kai ziyara Birtaniya......ku guji duk wani gangamin siyasa, gangami da wuraren wasanni. A guji wuraren cunkoson jama'a da manyan taruka," in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Nijeriya a shafinta na X.
Firaministan Birtaniya Keir Starmer na shirin gudanar da taron gaggawa a ranar Litinin bayan wasu masu tsattsauran ra'ayi sun soma zanga-zanga a faɗin Birtaniya a ƙarshen makon da ya gabata inda aka kama ɗaruruwan mutane.
"Rikicin ya dauki wani sabon salo mummuna, kamar yadda rahotanni suka nuna a hare-haren da ake kai wa jami'an tsaro da kuma lalata ababen more rayuwa," in ji gargadin kan tafiye-tafiye da Nijeriya ta yi.
'Yan sandan Birtaniya sun dora alhakin tashin hankalin a kan magoya bayan kungiyoyin da ke da alaka da kungiyar English Defence League, mai adawa da Musulunci da aka kafa shekaru 15 da suka gabata, wadda ake alaƙanta magoya bayanta da tayar da rikici a wuraren kallon kwallon kafa.
Kai hare-hare kan masu neman mafaka
Mummunan tashin hankali ya ɓarke a ranar Lahadi a Rotterham, a arewacin Ingila, inda wasu masu zanga-zanga da suka rufe fuska suka farfasa tagogi a wani otel wanda aka rinƙa amfani da shi a matsayin matsuguni ga masu neman mafaka.
An raunata aƙalla 'yan sanda 10, daga ciki har da wani wanda aka sumar, in ji 'yan sandan South Yorkshire.
Haka kuma an yi rikici sosai a Bolton, da ke arewa maso yammacin Ingila, da Middlesbrough da arewa maso gabashin Ingila, wanda wuri ne da masu zanga-zanga suka fasa gidaje da motoci da kuma kama mutum 43.