Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA ta ce ta kama kwayar methamphetamine da ta kai ta sama da naira miliyan 500 a filin jirgin Legas.
NDLEA ta bayyana cewa ta kama wannan kwaya ne a yayin da ake niyyar jigilarta zuwa kasar Ingila.
A sanarwar da hukumar ta fitar ranar Lahadi, ta ce an zuba miyagun kwayoyin a cikin robobin kunun kwastad masu yawa inda nauyin kwayoyin ya kai kilo 30.10.
Hukumar ta ce kwayar ta methamphetamine, wadda aka kama a ranar 16 ga watan Mayu, darajarta ta kai naira miliyan 567.
NDLEA ta kama wani da koken kunshe a cikin kwaroron roba a Nijeriya
Hukumar ta ce wannan kamen ya kai ta ga kama dillalin da ya yi niyyar safarar kwayoyin zuwa kasar Ingila mai suna Charles Chinedu Ezeh.
“Ezeh ya yi ikirarin cewa shi dan kasuwa ne a Onitsha, amma bincike ya nuna ya zauna shi da matarsa a da ‘ya’yansa a Landan har zuwa 10 ga watan Satumbar 2022 inda ya gudu zuwa Nijeriya bayan ya aikata laifin da ke da alaka da kwayoyi a Birtaniya,” in ji sanarwar.
Duk da ya yi ikirarin yana zaune a otel tun bayan komawarsa Nijeriya a Disambar bara, jami’an tsaro sun yi kokarin gano gidansa a Unguwar Lekki bayan an gudanar da bincike inda aka gano takardun tafiyarsa da kuma kayayyakinsa.
Ana yawan samun lamuran safarar miyagun kwayoyi a Nijeriya amma hukumar ta NDLEA ta ce tana samun ci gaba matuka wurin dakile wadannan ayyuka.
Ko a makon jiya sai da hukumar ta sanar da kama sama da mutum 500 da ake zargi da ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Haka kuma a cikin watan nan na Mayu hukumar ta ce ta kama tireloli biyu dauke da tabar wiwi a Legas da nauyinsu ya kai kilo 8,852.