Daga Seddiq Abou El Hassan
Da ya iya zama mafi kyau, laifin da aka kasa magance shi. Wadanda lamarin ya shafa ba ma sa iya bayani na kwakrewa da ake fahimta sosai, ballantana ma su rubuta munanan abubuwan da ake musu a litattafai.
Wannan shi ne misalin a kalla yadda azzalumai wadanda ba sa ganin aibu ko kadan wajen daukewa jama’a karfin ikonsu.
Dabbantar da wata al’umma ce hanya mafi sauki da za a lullube irin zaluncin da ake yi musu, sannan hana su bayyana al’adunsu na daya daga hanyoyin zaluncin.
Amma kuma abu ne da aka iya tunawa ba tare da kwarewar al’ummu da manyan malaman Yammacin Afirka na wancan lokacin ba.
Akwai misalai na kalubalantar hakan da dama, amma wadannan da za mu kawo sun fi jan hankali.
Hafizin Al-kur'ani Mai Girma da ke noman ciyawar taba
Ayyuba Suleiman Diallo ya zama babin nazarta kan makantar mulkin mallaka ga fasalin zamantakewar al’umma ‘yan asalin wani yanki.
Dan kasuwa da ya ga haja a banza ne kawai zai yi garkuwa da yin awon gaba da mutum mai ilimi kamar Ayyuba Suleiman, sannan ya sayar da shi ga masu noman ciyawar taba a Amurka don yin aikatau.
An haife shi a cikin al’ummar Fulani masu arziki, daga yankin Senegambia, mahaifinsa malamin addinin Musulunci ne da ake girmamawa kuma ya koyar da Ayyuba tare da sauran ‘ya’yansa.
Ya haddace Alkur’ani Mai Tsarki baki daya (Hakan ya sanya shi zama Hafizi) kuma ya fara taimaka wa mahaifinsa a lokacin da ya fara nuna kwarewarsa.
A 1731, an yi garkuwa da Diallo (Job Ben Solomon a majiyar Turai) inda aka tsallaka Tekun Atlantika da shi zuwa kasuwar bayi a tashar jiragen ruwa ta Annapolis da ke Maryland.
An raine shi don ya zama babban malami, babu abin da ya shirya shi a farkon rayuwarsa a Bondu don jure irin aikatau mai tsauri da ya tsinci kansa a ciki.
A tsawon rayuwarsa ta bauta, Diallo ya roki zama cikin imani. Bai taba hakura da ayyukan ibadarsa ba, yana sallah, duk da a wasu lokutan ana yi masa gatsali da cusguna masa.
Ya taba yin kokarin satar idanun iyayen gidansa ya gudu, amma aka kamo shi inda aka kai shi kurkuku.
Wannan koma baya ya sanya wani lauya dan Birtaniya jibintar lamarin.
Thomas Bluett ya saba da Diallo a lokacin da yake kurkuku, kuma sun dinga tattaunawa ta hanyar amfani da tafireta.
Abokan Diallo sun bayyana cewa ilimi da rikon addininsa ne suka janyo ana yi masa mu’amala ta daban da ta kowa, wanda hakan ne ya kai shi ga samun ‘yanci.
Amma kuma labarin ya bambanta idan aka kalli yadda bangaren Bluett ya bayar da shi.
Wani abun jin dadi a labarin shi ne minista ya yi kokarin jan ra’ayin masu gudanarwa don hada sanannen bawan da iyalansa.
“Bluett ya yi kokarin samun wasika daga cibiyar mulkin mallaka ta Maryland zuwa Bondu, wasikar da Suleyman Diallo ya rubuta da Larabci zuwa ga mahaifinsa inda yake neman taimakonsa kan ya dawo gida.
Bayan sauya hannu a tsakanin jami’an Birtaniya daban-daban, kuma ta gaza tsallaka Tekun Atlantika, a karshe wasikar ta shiga hannun James Oglethorpe, dan saurautar Birtaniya wanda ya gano Georgia a 1732.”
Amma akwai bayanin da ya fi karkakata ga kudi maimakon ga bauta. Oglethorpe wanda yana da ruwa da tsaki a harkokin ‘Royal Niger Company’ ya so amfani da matsayin da Diallo ke da shi a tsakanin al’umma, don ya samu damar isa ga albarkatun kasa da yankin Senegambia ke da shi.
Abun da wannan dan jari hujja ya kasa ganewa shi ne an raini Diallo bisa turbar Addinin Musulunci da muhawara ta addini, ba wai amincewa da wata yarjejeniyar samun abun duniya ba.
Idan zai yi rashin nasara a matsayin falke talaka, to kwarewarsa ta malanta ta bayyana a lokacin da yake tsallakawa zuwa Landan da tsawon rayuwarsa a Ingila.
Wadanda ke kewaye da shi sun gamsu da yin mamakin yadda wahalhalu na tsawon shekaru ba su lalata masa tunani ba.
Bluett, da cikin tsanaki ke ci gaba da sanya idanu kan halayen Diallo, ya bayyana cewa a 1734 Diallo ya rubuta kwafin Alkur’ani Mai Tsarki guda uku, ba tare da neman taimako daga wani kwafin ba, kuma ba ya kallon kowanne a lokacin da yake rubuta wani.
Amma abu mafi girma shi ne yadda ya tsaya tsayin daka wajen gudanar da Ibadunsa na Musulunci, duk da wahalhalu da ya dinga fuskanta.
A ruwayoyi daban-daban, Suleiman ya ci gaba da yin sallolinsa biyar a kowacce rana, ya ki shan giya, kuma yana cin naman da ya san ya Musulunci ya yarda a ci.
Bayan shekaru da dama, an ba shi dama ya dawo kasarsa, kuma ya sauya yanayin zamantakewa sosai.
Daga nan ne masu rubuta tarihinsa suka dinga zaucewa suna sumbatu, suna bayar da labaransa kamar yadda ake a kagaggun labaran karni na 18.
Wasu labaran ma na cewa a lokacin da ya zo Bondu, ya tarar mahaifinsa ya rasu, kuma matarsa ta sake aure.
Sai ya juya yana kira ga wasu abokansa da ke Ingila yana sanar da su kan halin da ya tsinci kansa, kuma yana rokon su taimaka masa kan yadda zai dawo Landan. Amma babu tabbaci ko sahihancin wannan kauli.
Sheikh Omar … Malamin Addini
Bayan karni daya, a Amurka da aka samu tsananin rarrabuwar kai kan bautar da mutane da kuma barkewar yakin basasa, wani dan gidan shugabannin Yammacin Afirka zai sake fuskantar irin wannan kaddara, amma shi tasa ta sha bambam.
Komai ya bayyana, matashi Omar bin Said ya zama babban malamin addini a garinsu na Futa Toro da ke Sanagal a yau.
A wancan lokacin, yana da matukar hatsari zama dan Yammacin Afirka.
A wuraren 1807, an yi garkuwa da shi tare da sayar da shi ga masu cinikin bayi zuwa Charleston, Carolina ta Kudu.
Bayan rashin nasarar tserewa, an kai shi kurkuku cikin matsanancin hali saboda kasancewar sa bawa da ya so ya gudu.
Da sai dai a kasa bayar da labarinsa na musamman, ba don ya jajirce wajen barin rubutu kan yadda ya taka sahun barawo ba game da laifin da ba shi ya aikata ba.
A jikin bangon dakin da aka daure shi a Fayetteville, ya fara rubuta wasu abubuwa na bangaren rayuwarsa ta baya, bisa dogaro kan abubuwan da yake iya tunawa.
A rubutun akwai muhimman bangarori na Alkur’ani, sannan ga ayoyi tare da addu’o’i da kuma yunkurin bayyana rashin jin dadinsa da yawaitar rasa nutsuwa.
Shafuka 12 da ya rubuta a takardar maghrib, ta hanyar amfani da rubutun Mahdara na Yammacin Afirka, wannan ne rubutun wani bawa da aka taba yi a Amurka, kamar yadda Cibiyar adana tarihi a zamanance ta ‘Lowcountry Digital History Initiative’ ta bayyana.
Saboda yadda a wannan yanayi na yadda mai gidan bawa ba zai iya karanta Larabci ba, ba a iya tace rubutun ba, kuma haka ya isa ga al’ummun da suka biyo baya wanda ba kasafai aka cika samun rubutun da ba a tantance shi ba kan bautar da ‘yan Afirka, inji Mary-Jane Deeb, shugabar sashen Gabas ta Tsakiya da Afirka a dakin karatu na Majalisar Dokokin Amurka.
Duk da karfin kwakwalwarsa ya ragu ga kuma alamun razani, amma takardun da ya rubuta sun isa zama shaidar kawar da duk wata karya kan yadda kasuwancin bayi yake samun tagomashi daga jama’a jahilai, wadanda ba su da wayewa, da za a bautar da su.
Takardun masu daraja da aka bai wa sunan ‘Rayuwar Omar bin Said’ a yanzu haka suna nan a dakin Karatu na Majalisar Dokokin Amurka.
A 1860 ne sanannen dan gwagwarmayar neman hana bautar da mutane Theodre Dwight ya yi aiki mai gajiyarwa don tattara wannan rubutu waje guda.
Amma kuma rubutun ya sauya daga hannu zuwa hannu a lokuta da dama, kuma ya bata na tsawon shekaru amma aka sake gano shi, an kuma dan lalata shi.
Bayanan da aka adana a zamanance sun nuna yadda rayuwar Omar ta inganta bayan da wasu iyalai masu karfin fada a ji da hannu da shuni suka saye shi tare da kai shi Carolina ta Arewa da nufi mayar da shi Kirista nagartacce.
Duk da mutanen sun gamsu da malamin na Musulunci ya karbi Kiristanci, amma ta bayyana karara yadda yake ajiye Bible dinsa, kuma ya kan kawo misali ma daga Alkur’ani Mai Tsarki a yayin karanta shi.
Watakila ya yi rayuwa da addinai biyu ne, ko kuma ya karbi Kiristancin ne don kar ya batawa iyayen gidansa rai.
Bayan sama da shekara 50 a matsayin bawa, Omar ya mutu a 1864, shekara guda kafin Amurka ta haramta bautar da mutane da kasuwancin bayi.
Shin da wanne irin mutum zai zama da a ce ba a yi garkuwa da shi ba a ranar kaddara a shekarar 1807?