Gwamnatin Amurka ta gargadi ‘yan kasarta a kan yin tafiye-tafiye zuwa Uganda inda ta ce kasar na fuskantar barazanar rikici sakamakon laifuka da ta’addanci da kuma kin jinin dokar ‘yan luwadi da madigo.
Sai dai wannan bai zo da mamaki ba ga jama’a da dama.
Amurka ta sha bayar da irin wadannan shawarwari lamarin da masu sharhi ke kallo a matsayin mara ma’ana.
“Wadannan shawarwari wadanda kasashen yamma ke bayarwa ba su da amfani,” in ji Dakta Adams Bornah, masani kan harkokin tsaro a Ghana.
“Suna bayar da wadannan shawarwari duk bayan watanni uku ko kuma shida, amma ba abin da aka fasa.
Suna jawo rudani ne kawai kuma mutane na ci gaba da tafiya zuwa kasashen da aka ba su shawara kada su je,” a cewar masanin.
‘Laifi tudu ne’
Kasashe na bayar da shawarwari kan tafiye-tafiye inda suke gargadin ‘ya'yansu game da wuraren da suka kamata su je da kuma wadanda ba su kamata su je ba.
Suna gargadi kan yadda mutum ya kamata ya tafiyar da rayuwarsa a wasu wurare ko a tare da wasu mutane bayan sun yi bincike kan yanayin tsaron wuraren.
Sai dai wasu kasashen yamma, musamman Amurka, sun sha bayar da shawarwari bagatatan, inda a wani lokaci ake dasa ayar tambaya kan ainihin manufar bayar da shawarwarin.
Dakta Adams ya ce lamarin da suke gargadi a kai ya fi muni a kasarsu fiye da wuraren da suke cewa kada a je.
"Misali, suna shaida wa mutane cewa kada su kuskura su je wasu sassan Afirka, amma kun san abin da ke faruwa a New York ko Washington DRC?
Rikicin da ake yi ya fi wanda ke faruwa a Burkina Faso. Suna da kalubalensu da ya kamata su mayar da hankali a kai.”
Kamar yadda ya kara da cewa. “Akwai matsaloli da dama da suka shafi rikicin amfani wuka a London fiye da Somalia."
Gwamnatin Nijeriya da Afirka ta Kudu a bara sun mayar da martani ga wasu kasashen yamma, ciki har da Amurka, a lokacin da suka gargadi ‘yan kasashensu kan tafiya wasu sassan Nijeriya har da Abuja da wasu sassan Afirka ta Kudu.
Amurka ta bayar da shawarwari sama da sau 40 a cikin shekara guda kan tafiye-tafiye a wasu kasashen duniya.
Yin biyayya
Sai dai kamar yadda mai sharhi kan tsaro Dakta Adams ya bayyana, mutanen da suke ikirarin suna karewa ba su yarda da maganganunsu ba.
“Ka je arewacin Nijeriya kawai, ko kuma wasu sassa na Kamaru da Somalia, za ka ga Amurkawa nawa ne ke wurin. Ba za ka iya hana mutane yawo ba,” in ji Dakta Adams.
Masu sharhi kuma sun kara da cewa wadannan shawarwarin wata hanya ce ta dakile kasashe masu tasowa domin yin biyayya ga tsare-tsarensu da kuma tsoratar da masu son zuba jari – inda hakan ke kawo cikas wurin ci-gaban tattalin arzikinsu.
“A ganina wadannan mutanen na kawo rudani ne kawai inda suke amfani da batun tsaron,” in ji Dakta Adams.
“Idan ka ki amincewa da su ko kuma ka nuna cewa ba ka son ka yi biyayya, sai su fito da irin wadannan maganganun domin taimaka musu cimma burinsu.”
Nuna jajircewa
Sabbin shawarwarin tafiye-tafiyen da Amurka ta yi sun tabo batun dokar da ‘yan majalisar Uganda suka zartar ta yanke hukunci mai tsauri ga ‘yan luwadi.
Sai dai Shugaba Museveni ya sha dagewa inda yake kare dokokin da kasar ta yi na ayyana luwadi da madigo a matsayin laifi.
Kamar yadda mai sharhi kan tsaro Dakta Adams ya bayyana, dole ne shugabannin Afirka su rinka jajircewa kan matakansu duk da tsoratarwa daga kasashen da ke tunanin suna da karfi.
Kasashen yamma irin su Amurka ‘ba su da tsaron’ da suke ikirarin suna da shi.