Sai dai duk da haka ba a bude harkar sufurin saman ga duk wasu ayyukan jiragen soji ba, ta yadda sai sun nemi izini daga hukumomin da suka kamata tukunna. Hoto: Reuters

Nijar ta bude sararin samaniyarta wata daya bayan rufe shi da ta yi sakamakon juyin mulkin da aka yi a watan Yuli.

Sojojin Nijar sun rufe sararin samaniyar kasar ne bayan da suka kwace mulki a ranar 26 ga watan Yuli, sai suka bude shi ranar 2 ga watan Agusta, sannan a ranar 6 ga Agustan kuma sai suka sake rufe shi bayan da kasashen yammacin Afirka suka yi barazanar amfani da karfin soji don mayar da mulkin farar hula a kasar.

Mai magana da yawun ma'aikatar sufuri na Nijar ya shaida wa kamfanin dillancin labaran kasar ANP cewa bayan hakan an kuma dawo da sufurin motoci.

Sai dai duk da haka ba a bude harkar sufurin saman ga duk wasu ayyukan jiragen soji ba, ta yadda sai sun nemi izini daga hukumomin da suka kamata tukunna.

Barazanar amfani da karfin soji

Kungiyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma ta kakaba takunkumai a kan Nijar bayan hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum sannan ta yi barazanar amfani da karfin soji a matsayin mafita ta karshe wajen warware matsalar idan har aka gaza sasantawa wajen mayar da mulkin farar hula.

A ranar 2 ga watan Agusta ne Nijar ta sake bude kan iyakokinta na kasa da kasashe biyar da suka hada da Aljeriya da Burkina Faso da Libya da Mali da kuma Chadi.

An bai wa wasu jiragen izini na musamman don ci gaba da aiki da filin jirgin sama na Niamey.

A ranar Juma'a ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akwai dumbin tan-tan na abinci da za a kai Nijar amma sun makale saboda rufe iyakoki.

AFP