Dangantaka tsakanin Nijeriya da maƙwabciyarta Nijar ta yi tsami tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar a 2023. / Hoto: Nigeria Presidency

Gwamnatin Nijeriya da kakkausar murya ta yi watsi da zargin da gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta yi kan cewa Nijeriyar ta zama wani sansani na musamman domin kawo hargitsi a ƙasar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriyar ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.

A ranar Alhamis da maraice ne dai Ministan Harkokin Wajen Nijar ɗin ya gayyaci gayyaci jami’a mai kula da harkokin diflomasiyya a ofishin jakadancin Nijeriya da ke ƙasar domin ta yi ƙarin bayani.

Sai dai a sanarwar da Nijeriyar ta fitar, ta bayyana matuƙar damuwarta kan lamarin inda ta ce ba gaskiya ba ne.

“Gwamnatin Nijeriya ta nuna matukar damuwarta tare da bayyana cewa babu sojojin Faransa a yankin arewacin kasar da ke shirin hargitsa gwamnatin Nijar. Wadannan zarge-zarge ba su da tushe kuma ya kamata a yi watsi da su baki daya,” kamar yadda sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta bayyana.

Bayan haka kuma, gwamnatin Nijeriyar ta yi watsi da wani zargi da gwamnatin Nijar ɗin ta yi kan cewa ‘yan ta’addan Lakurawa da taimakon jami’an tsaron ƙasashen waje, ciki har da na Nijeriya na da hannu a harin da aka kai kan bututun mai na Nijar-Benin a ranar 13 ga watan Disambar 2024 a Gaya da ke yankin Dosso na Jamhuriyar Nijar.

Haka kuma gwamnatin ta Nijeriya ta miƙa saƙon jajenta kan lamarin da ya faru na hari kan bututun man.

Dangantaka tsakanin Nijeriya da maƙwabciyarta Nijar ta yi tsami tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar a 2023.

TRT Afrika