Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda yara da dama sun rasu a Jihar Oyo a wani turmutsutsu yayin wani bikin bai wa yara 5000 kyautar naira dubu biyar-biyar. / Hoto: NPF

Aƙalla mutum goma ne suka rasu a yayin wani turmutsutsu da ya faru a wurin rabon kayan Kirisimeti a Abuja.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar da safe a Cocin Holy Trinity da ke unguwar Maitama a Abuja babban birnin ƙasar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Abuja babban birnin ƙasar Josephine Adeh ce ta tabbatar da lamarin inda ta ce lamarin ya faru ne da misalin 6:30 na safe inda mutum goma suka rasu sannan takwas suka jikkata a wurin rabon kayayyakin abinci.

Ta bayyana cewa daga cikin waɗanda suka rasu har da yara huɗu. Haka kuma ta bayyana cewa daga cikin mutum takwas ɗin da suka jikkata, an sallami huɗu daga asibiti inda sauran kuma ke ci gaba da samun kulawa.

Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda yara da dama sun rasu a Jihar Oyo a wani turmutsutsu yayin wani bikin bai wa yara 5000 kyautar naira dubu biyar-biyar a filin wasan makarantar boko ta Islamic High School a unguwar Bashorun da ke Ibadan.

Tuni gwamnan jihar Seyi Makinde ya bayar da umarnin kama mutanen da suka shirya wannan bikin.

TRT Afrika