Shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya ce za su kare nasarorin da suka wahala wurin samu a kasar.
Ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter ranar Alhamis awanni bayan sojoji sun sanar da kifar da gwamnatinsa.
"Za a kare nasarorin da aka sha wahala wurin samunsu. Dukkan 'yan Nijar da ke kaunar dimokuradiyya za su ga hakan," in ji sakon na Bazoum.
Shi ma Ministan Harkokin Wajen Nijar Hassoumi Massoudou ya wallafa sakon Twitter inda ya yi kira ga duk masu kaunar dimokuradiyya da kishin kasa su tashi tsaye don kare ta.
''Ina kira ga dukkan masu kaunar dimokuradiyya da 'yan kishin kasa su murkushe" barazanar da kasar take fuskanta.
Mr Massoudou ya bayyana kansa a matsayin 'shugaban rikon kwarya na gwamnati.'
Ranar Laraba sojojin Jamhuriyar Nijar suka sanar da kifar da gwamnatin farar-hula ta Shugaba Bazoum.
Sojojin sun bayyana haka ne a wata sanarwa da suka karanta a wani gidan talabijin na kasar da tsakar dare.
Sun ce an rufe dukkan iyakokin kasar sai abin da hali ya yi, sannan suka sanya dokar hana fita a kasar.
“Mu, dakarun tsaro mun yanke shawarar kawo karshen gwamnatin Shugaba Bazoum,” in ji jagoran sojojin Laftanar Kanar Amadou Abdramane.
Yana bayanin ne kewaye da wasu sojoji tara. Ya kara da cewa “an soke dukkan hukumomi" na tsarin mulki a kasar.
Wannan lamari ya faru ne bayan sojoji da ke kula da fadar shugaban kasar sun toshe fadar shugaban kasar da gidansa da ke Yamai babban birnin kasar ranar Laraba da safe.
Kasashe da manyan hukumomin duniya na ci gaba da yin tir da matakin da sojojin Nijar suka dauka.