A ranar Laraba da tsakar dare ne sojoji a Jamhuriyar Nijar suka sanar da kifar da gwamnatin farar-hula ta Shugaba Mohamed Bazoum.
Sojojin sun bayyana haka ne a wata sanarwa da suka karanta a gidan talabijin na kasar inda suka ce an dakatar da duk wata hukuma ta dimokuradiyya sannan sun sanya dokar hana fita a kasar.
Kasashe da kungiyoyi sun yi tir da wannan lamari ciki har da Kungiyar Tarayyar Afirka da ECOWAS da Kungiyar Tarayyar Turai har ma da Majalisar Dinkin Duniya.
Ga dai wasu abu biyar da suka kamata ku sani game da Nijar, wacce ke yankin Afirka ta Yamma da ke da dimbin arzikin makamashin yuraniyom.
1. Juyin mulki hudu
Nijar ta sha fama da rikicin siyasa tun bayan da ta samu 'yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.
Sau hudu kasar na fama da juyin mulki a tarihinta, na baya-baya shi ne na watan Fabrairun 2010 wanda ya yi sanadin hambarar da shugaban kasar na wancan lokacin Mamadou Tandja.
A shekarar 2021 ne aka mika mulki na farko daga farar-hula zuwa farar-hula, lokacin da Mohamed Bazoum ya karbi ragamar mulkin daga Mahamadou Issoufou, bayan gudanar da zabe.
2. Albarkatun kasa na yuraniyom, zinare da fetur
Nijar na daya daga cikin kasashen duniya da suka fi arzikin yuraniyom, wanda shi ne babban sinadarin da ake amfani da shi a masan'antar samar da makamashin nukiliya.
Faransa, wacce take samun kusan dukkan lantarkinta daga tasoshin nukiliya, ta fara hakar yuraniyom a arewacin Nijar tun shekara 50 da suka wuce.
Kazalika kasar ta kuma zama wata karamar mai fitar da zinare da fetur.
Sai dai mafi yawan al'ummarta sun dogara ne da noma.
3. Rabin al'ummar kasar na rayuwa cikin talauci
Nijar, wacce ke da girman kasa fiye da kowace kasa a Afirka ta Yamma, in da girmanta ya kai kashi biyu cikin uku na sahara, tana daga cikin kasashen duniya da suka fi fama da talauci.
Rabin al'ummarta miliyan 26.2 na rayuwa ne cikin talauci, a kasar da aka kiyasta cewa akalla kowace mace kan haifi yara shida a shekarar 2021, a cewar hukumomi.
Kamar sauran kasashen da suke yankin Sahara, ita ma Nijar tana asarar kasarta mai albarka noma sakamakon kwararar hamada, lamarin da ke yawan jawo fari da yunwa.
Tana cikin shirin Afirka na Great Green Wall, wanda ke burin dasa bishiyoyi da tsirrai na tsawon kilomita 8,000 a lungu da sako na nahiyar.
4. Tagwayen masu ta da kayar baya
Nijar kasa ce da ke makwabtaka da kasashen Nijeriya, Mali da Burkina Faso, tana fama da matsalar masu tayar da kayar baya da ta faro a Mali a shekarar 2012 yadda ta bazu zuwa yankin sakamakon rashin isasshen tsaro a kan iyakokin kasashen.
Rikicin kungiyoyin Boko Haram, Al-Qaeda da IS ya shiga kasar har kusan kilomita 100 daga babban birninta.
Mafi muni daga cikin hare-haren da suka taba faruwa shi ne wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 141 a yankin Tahoua a watan Maris din 2021, kamar yadda alkaluman hukumomi suka nuna.
Amurka na daga cikin kasashen da ke taimaka wa Nijar a wannan yaki da ta'addanci da ba a saba gani ba a yankin.
Faransa ma ta jibge dakaru 1,500 don yaki da ta'addanci a Nijar bayan da ta fice daga Mali da Burkina Faso.
5. Garuruwan gishiri
Arewa maso gabashin Nijar ya kasance wani yanki mai garuruwan da ke da tarin gishiri
Har yanzu ba a gano asalin wasu duwatsu da tsaunkuna da katangu na "kasar" da ke Djado ba.
Nijar na neman Hukumar Tarihi da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanya yankin a cikin kundinta.